Hukumar Kula da Manyan Hanyoyi, Ghana
| Bayanai | |
|---|---|
| Iri |
government agency (en) |
| Ƙasa | Ghana |
| Mulki | |
| Hedkwata | Accra |
| Tarihi | |
| Ƙirƙira | 1974 |
An kafa hukumar (GHA), bisa dokar GHA Degree 1974 (NRCD 298). Dokar GHA ta 1997 (Act 540), ta soke NRCD 298, wadda, duk da haka, kungiyar ta ci gaba da gudanarwa, sarrafawa, ci gaba, gami da kula da hanyar sadarwa ta ƙasar. Manyan hanyoyin ƙasar, na da jumullar tsawon nisan kilomita 13,367 gaba-dayan su, hakan ya kai kusan kashi 33% na jimlar hanyoyin sadarwa na fadin ƙasar ta Ghana da ke da jumullar tsawon nisan kilomita duba 40,186. [1][2]
Sashe
[gyara sashe | gyara masomin]Dukkanin wasu ɓangarorin sassan hukumar an haɗa su a ƙarƙashin babban sashen da aka kasa gida uku, wato:
- Ma'aikatar Gudanarwa
- Ma'aikatar Ci Gaba
- Ma'aikatar Kulawa
Ma'aikatar Gudanarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Wannan Ma'aikatar ta ƙunshi rabe-rabe 7, ga su kamar haka:
- Kudi
- Albarkarun ƙasa
- Ayyukan Shari'a
- Horarwa da Ci gaba
- Harkokin Jama'a
- Sashen MIS
Akwai Sashen Bincike na Cikin Gida, wanda ke da alhaki by na kai tsaye ga Babban Darakta amma wanda domin dalilai na gudanarwa, yana bayar da rahoto ga Mataimakin Babban Daraktoci (Administration). [3]
Ma'aikatar Ci Gaba
[gyara sashe | gyara masomin]Wannan Ma'aikatar ta kunshi rabe-rabe ƙwaya 7, wato:
- Tsaro da Muhalli
- Shirye-shiryen
- Kayan aiki
- Yarjejeniya
- Bincike
- Bincike da tsari
- Gadoji
Shugaban wannan Ma'aikatar shine Mataimakin Babban Darakta na Ci Gaba.
Ma'aikatar Kulawa
[gyara sashe | gyara masomin]Wannan Ma'aikatar ta ƙunshi:
- Kula da Hanyoyi
- Ofisoshin Yankin (kwara 10 , ɗaya a kowane yanki)
- Shuka da Kayan aiki
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Site Admin. "About GHA". Archived from the original on 28 July 2013. Retrieved 21 July 2013.
- ↑ "PWDs at toll booths cry over unpaid salaries". BusinessGhana. Retrieved 2020-01-11.
- ↑ "Admin Department". Site Admin. Archived from the original on 28 July 2013. Retrieved 22 July 2013.