Jump to content

Hukuncin kisa a Malta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hukuncin kisa a Malta
aspect in a geographic region (en) Fassara
Bayanai
Fuskar hukuncin kisa
Ƙasa Malta

An soke Hukuncin kisa saboda kisa a ƙasar Malta a shekarar 1971. Sai dai hukuncin kisa ya ci gaba da kasancewa a cikin dokar soja ta ƙasar har sai da aka soke shi gaba ɗaya a ranar 21 ga Maris, 2000. Malta na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaɓi ta Biyu ta Ƙungiyar Ƙasashen Duniya kan 'Yancin Dan Adam da Siyasa, wadda ke wajabta soke hukuncin kisa a cikin iyakokin ƙasar. Haka kuma, Malta ta amince da ƙa'ida ta 13 ta Yarjejeniyar Turai kan 'Yancin Dan Adam, wadda ke haramta hukuncin kisa a kowane hali.

An aiwatar da hukuncin kisa sau goma sha takwas (18) a tsakanin shekarun 1876 da 1943. Kisan ƙarshe ya faru ne a ranar 5 ga Yuli, 1943, inda aka rataye 'yan uwan nan Karmnu da Guzeppi Zammit saboda laifin kisan Spiru Grech.

Hukuncin kisa na ƙarshe da ba don kisan kai ba ya gudana ne a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, lokacin da aka rataye Carmelo Borg Pisani saboda laifin cin amanar ƙasa a ranar 28 ga Nuwamba, 1942. Pisani mutumin asalin Malta ne wanda ya shiga jam’iyyar fasist ta ƙasar Italiya (Italian National Fascist Party) kuma ya karɓi ɗan ƙasar Italiya a shekarar 1940. Ya dawo Malta ne domin gudanar da aikin leƙen asiri a shirye-shiryen mamayar tsibirin daga ɓangaren ƙungiyar Axis.

Mutum na ƙarshe da aka yanke wa hukuncin kisa a Malta shi ne Anthony Patignott, a ranar 1 ga Oktoba, 1963, saboda kisan Manwel Baldacchino. Gwamna Janar na Malta a wancan lokaci, Maurice Henry Dorman, ya sauya hukuncin kisansa zuwa ɗaurin rai da rai.

Ra’ayin jama’a a Malta yana da ƙarfi wajen adawa da hukuncin kisa. Binciken European Values Study (EVS) na shekarar 2008 ya nuna cewa kashi 70.3% na masu amsa tambayoyi a Malta sun ce hukuncin kisa ba zai taɓa zama daidai ba, yayin da kashi 4.5% kawai suka ce ana iya halatta shi a kowane lokaci.[1]

  1. "GESIS: ZACAT". zacat.gesis.org. Retrieved 2019-06-19.