Hukuncin kisa a yankin Tekun Indiya na Burtaniya
|
aspect in a geographic region (en) | |
| Bayanai | |
| Fuskar | hukuncin kisa |
| Ƙasa |
British Indian Ocean Territory (mul) |
Hukuncin kisa a Ƙasar Yankin Tekun Indiya na Burtaniya (British Indian Ocean Territory) ba a yarda da shi ba a ƙarƙashin dokar cikin gida ta ƙasar, daidai da matsayar duk sauran Yankunan kasashen waje na Burtaniya.
A ƙarƙashin sharuɗɗan wata yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa da aka kulla a shekarar 1966,[1] yawancin mazauna Tsibirin Birtaniya na Indiya (BIOT) mambobi ne na rundunar sojin Amurka, kuma suna ƙarƙashin dokokin soja na Amurka dangane da laifukan da suka aikata, wanda ke ba da damar yanke hukuncin kisa. Sai dai yarjejeniyar ta kuma bayyana cewa: “Ba za a aiwatar da hukuncin kisa a cikin wannan yanki ta hannun hukumomin sojin Amurka ba.[2]
Ga mutanen da suke ƙarƙashin dokar laifuka ta Tsibirin Birtaniya na Indiya wanda galibi ya shafi masu gudanarwa da baƙi da ke cikin ruwan yankin BIOT dokar koto 1983 ta tanada cewa,[3] a mafi yawan lokuta kuma idan babu wata doka ta musamman a yankin da ta shafi batun, dokar BIOT za ta kasance daidai da "dokar Ingila yadda take aiki a kowane lokaci a Ingila".
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "D16b1: U.S./U.K. BIOT agreements, 1966-1987 (Bancoult v. McNamara, D.D.C., No. 01-CV-2629)". Archived from the original on July 16, 2012. Retrieved February 18, 2015.
- ↑ "Annex 2, Paragraph 1(g)" (PDF). UN Treaty Series: 286. 1967. Retrieved 16 June 2020.
- ↑ British Indian Ocean Territory Ordinance No. 3 of 1983 ("the Courts Ordinance"), Article 3.1.