Hussain Salihu
An haifi Hussain Egyegbola Salihu ranar 29 ga watan Yuni, shekarar 1959 a kauyen Agwatashi dake karamar hukumar Obi a jihar Nasarawa. Dan asalin jihar Nasarawa ne kuma shine Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Kudu.[1]
Farkon Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Hussain ya halarci makarantar Sakandare ta Mada Hius inda ya samu shaidar kammala karatunsa na sakandare (WAEC) a shekarar 1978 sannan ya wuce Jami'ar Ahmadu Bello inda ya yi digirin farko a fannin Architecture a shekarar 1982. A shekarar 1984 ya ci gaba a Jami'ar Ahmadu Bello don yin digirinsa na biyu a fannin fasahar kere kere. Ya kuma sami takardar shaidar kammala karatun digiri a cikin Gudanarwa daga Jami'ar Jos a 1992.
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]A zaben 2015, Salihu ya tsaya takarar kujerar Sanatan Nasarawa ta Kudu a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.[2]
Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party,(PDD) kuma Sanata mai ci, Sanata Suleiman Adokwe Ya kalubalanci Nasarar Salihu a Kotun Saurraron kararrakin zabe ta jihar Nasarawa, daga baya kotun ta yi watsi da karar da ya shigar a gaban ta ya daukaka kara a kotun da ke Markudi a jihar Benue, inda kotun ta tabbatar da nasarar zaben Sanata Adokwe sannan ta umarci INEC da ta mayar da Sanata Adokwe a matsayin zababben sanata mai wakiltar Nasarawa ta Kudu.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-11. Retrieved 2023-07-11.
- ↑ https://www.manpower.com.ng/people/15513/hussain-salihu