Jump to content

Ibrahim Kefas

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ibrahim Kefas
Gwamnan jahar delta

26 Satumba 1994 - 22 ga Augusta, 1996
Bassey Asuquo - John Dungs
Gwamnan jihar Cross River

9 Disamba 1993 - 14 Satumba 1994
Clement Ebri (en) Fassara - Gregory Agboneni
Rayuwa
Cikakken suna Ibrahim Kefas
Haihuwa 27 ga Janairu, 1948
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Mutuwa 1 Oktoba 2021
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Air Commodore (mai ritaya) Ibrahim Kefas (27 Janairu 1948 - 1 Oktoba 2021) ya yi aiki a matsayin mai kula da soja na Jihar Cross River a Najeriya tsakanin Disamba 1993 da Satumba 1994, sannan kuma na Jihar Delta har zuwa Agusta 1996 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha. [1]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ibrahim Kefas acikin iyalin Kirista a ranar 27 ga watan Janairun 1948, a Wukari, Jihar Taraba. Shi ne babba a cikin yara da yawa da Christian missionary Atewunu Angyu Kefas (Manu) ya haifa. Mahaifinsa, Manu, yana ɗaya daga cikin masu wa'azin mission da suka gabatar da addinin Kiristanci a yankin. Da yake shi Kirista ne mai kishin addini, ya sanya Ibrahim Kefas a Kwalejin Bible tun yana da shekaru goma sha uku yana fatan ya zama mai wa’azi. Ibrahim Kefas, kasancewar shi ne dalibi mafi karancin shekaru a Kwalejin Bible a lokacin, ya kammala karatu kafin yawancin su amma yana da wasu tsare-tsare. Jirage suna burge shi kuma yana so ya tuka su sai ya shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya ya zama matukin jirgi kafin ya cika shekara 20 a duniya.

A matsayin sa na Captain ɗin kungiya, an nada Kefas a matsayin gwamnan jihar Delta a ranar 26 ga watan Satumba 1994. [2]

Yayin da yake gwamnan jihar Delta, ya kori Farfesa Frank Mene Adedemiswanye Ukoli, mataimakin shugaban jami'ar jihar Delta saboda dalilai na siyasa, wani lamari da aka rubuta a littafin Ukoli A state university is born: throes of birth, ordeals of growth. [3]

A watan Maris na 2002, yayin da wasu matasa sama da 200 suka kai wa shugaban jam'iyyar PDP na jihar Taraba, Kefas da wasu 'yan siyasa hari, inda suka kutsa kai cikin taron jam'iyyar, da kyar suka tsira daga mutuwa.

An zabi Kefas ne a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar National Democratic Party a zaben 2007 a jihar Taraba. [4] Wanda ya lashe zaben shi ne dan takarar jam’iyyar People’s Democratic Party, Danbaba Suntai.

Kefas ya mutu ne a safiyar ranar 1 ga watan Oktoba, 2021, a wani asibiti a Abuja.

  • Jerin sunayen gwamnonin jihar Cross River
  1. "Nigeria States". World Statesmen. Retrieved 22 March 2010.
  2. "Delta State Economic Empowerment and Development Strategy" (PDF). Delta State Government. Archived from the original (PDF) on 24 July 2011. Retrieved 22 March 2010.
  3. Jike, Victor (28 January 2005). "F.M.A. Ukoli: An Obeisance". Retrieved 22 March 2010.
  4. "Independent National Electoral Commission Nominated Candidates for Governorship Election 2007" (PDF). Independent National Electoral Commission. Archived from the original (PDF) on 3 October 2007. Retrieved 22 March 2010.