Ibrahim Zakaria (mai haɗin gwiwar kwadago)
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Sudan, 1929 |
| ƙasa | Sudan |
| Mutuwa | 1993 |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan kasuwa |
Ibrahim Zakaria (17 Maris 1929 - 2 Nuwamba 1993) ya kasance dan kungiyar kwadago ne na kasar Sudan kuma mai fafutukar kwaminisanci.
Rayuwarsa ta farko da aikinsa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ibrahim zakaria a arewacin kasar Sudan a cikin dangin manoma, Zakaria ya yi karatun sa a Makarantar Fasaha ta Atbara kuma ya sami aiki a kan hanyoyin jirgin ƙasa na ƙasar. Ya shiga ƙungiyar kwadago, kuma ya kasance babba wanda ya kafa Ƙungiyar Ma'aikata a Kasar Sudan. A shekarar 1946, ya kasance daya daga membobin da suka kafa Jam'iyyar Kwaminisanci ta Sudan, yayi aiki a matsayin mai shiryawa a farko, ya kuma yi aiki da Kwamitin jam'iyyar mulkin mallaka.[1][2] A shekarar 1957, Zakaria ya koma Prague, don yin aiki da Ƙungiyar Kwadago ta Duniya (WFTU), a matsayin sakataren nahiyar Afirka. Wannan yana daya daga Cikin muhimmiyar rawa da ya taka, saboda ƙungiyoyin 'yancin kai a ƙasashe da yawa wato (WFTU) da fatan samun sabbin abokan hulda a Afirka sannan kuma su karfafa alakar su.[3] A shekarar 1973, ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa Ƙungiyar Kwadago ta nahiyar Afirka.[1] A shekarar 1980, Zakaria ya zama Babban Sakatare na WFTU, kuma an nada shi a matsayin babban shugaba na dindindin a shekarar 1982. A wannan mukamin da ya rike, ya wakilci kungiyar WFTU a Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Kwadago ta Duniya. A cikin shekarar 1990, Zakaria ya kuma zama shugaban kungiyar WFTU. Zakaria ya mutu a shekarar 1993, a kasar Prague.[1][2]