Igor Jesus
![]() | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| Haihuwa |
Cuiabá (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| ƙasa | Brazil | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| Tsayi | 180 cm | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Igor Jesus Maciel da Cruz (an haife shi 25 ga watan Fabrairu, 2001), wanda aka fi sani da Igor Jesus, ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Brazil wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba a ƙungiyar Serie A Botafogo da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brazil.[1]
Aikin Kungiya
[gyara sashe | gyara masomin]Igor Jesus ya zo ta hanyar matasa a Coritiba, tun yana da shekaru 13 a kungiyar. An ba shi matsayi a sashen manyan en wasa a cikin 2019, kuma ya fara buga wasansa na farko a matsayin wanda zai maye gurbin ranar 23 ga Janairu 2019, a wasan Campeonato Paranaense da Maringá. Ya ci kwallonsa ta farko a farkon fara wasa a ƙungiyar, a gasar guda daya a ranar 30 ga Janairu 2019 da Athletico Paranaense. A ranar 18 ga Maris 2019 ya rattaba hannu kan sabuwar kwangila, yana kiyaye haƙƙinsa tare da Coritiba har zuwa ƙarshen 2022. Ya yi wasansa na farko a gasar lig na ƙasa a wasan 2019 Campeonato Brasileiro Série B da CRB a ranar 20 ga Mayu 2019.[2]
A ranar 7 ga Yuli, 2024, bayan wata doguwar tafiya a waje tare da Shabab Al Ahli, Igor Jesus ya koma gida ya sanya hannu kan yarjejeniyar dindindin da kungiyar Botafogo.[3]
Aikin kungiyar Kasa
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin Oktoba 2024, Igor Jesus ya sami kiransa na farko zuwa tawagar 'yan wasan Brazil don wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 da Chile da Peru.[4]
Lambar Yabo
[gyara sashe | gyara masomin]A kungiyar Shabab Al-Ahl
[gyara sashe | gyara masomin]- UAE Pro League: 2022–23
- UAE President's Cup: 2020–21
- UAE League Cup: 2020–21
- UAE Super Cup: 2020, 2023
A kungiyar Botafogo
[gyara sashe | gyara masomin]- Série A: 2024
- Copa Libertadores: 2024
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://globoesporte.globo.com/pr/futebol/times/coritiba/noticia/louzer-lamenta-chances-perdidas-pelo-coritiba-contra-o-crb-pagamos-um-preco-caro.ghtml
- ↑ https://globoesporte.globo.com/pr/futebol/times/coritiba/noticia/primeiro-atletiba-primeiro-gol-atacante-igor-jesus-vive-noite-especial-pelo-coritiba.ghtml
- ↑ https://globoesporte.globo.com/pr/futebol/times/coritiba/noticia/igor-jesus-e-luizinho-estreiam-no-coritiba-e-passam-a-ser-alternativas-para-argel.ghtml
- ↑ https://fdp.fifa.org/assetspublic/ce233/pdf/SquadLists-English.pdf
