Jump to content

Ilimin likita a Najeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ilimin llikita a Najeriya
education in country or region (en) Fassara
Bayanai
Farawa 1948
Ƙasa Najeriya

Ilimin likitanci na farko a Najeriya ya fara ne a shekarar 1948 a birnin Ibadan, gaba-ɗaya ko kacokan ya ta'allaka bisa tsarin karatun Burtaniya. Tun daga wannan lokacin, makarantun likitanci sun faɗaɗa a faɗin ƙasar, kuma jami'o'in likitanci a yanzu suna ci-gaba da wanzuwa a kusan kowace jiha, ciki har da jami'o'in tarayya, jihohi dama masu zaman kansu. Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), da ƙungiyar likitoci da hakori ta Najeriya (MDCN) ne ke kula da ilimin likitanci a Najeriya.

Farkon fari

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 1927, gwamnati ta kafa shirin difloma na shekaru biyar don horar da ma'aikatan kiwon lafiya; amman shirin bai yi tasiri ba saboda malamai da kayan aiki ba su wadata ba don horar da likitoci kan matakan da aka yarda da su daga ƙasashen ƙetare. [1] An horar da likitocin ne kawai a Najeriya kuma an ba su sharuɗɗa na yin hidima idan aka kwatanta da likitocin da aka horar da su daga kasashen waje; rashin tasirin shirin a ƙarshe ya kai ga soke shirin. [2] A shekarar 1948, aka kafa reshen kwaleji na Jami'ar Landan a Ibadan, kuma za a horar da waɗanda suka kammala karatu daidai da takwarorinsu na Biritaniya tare da bayar da digiri na Jami'ar London a kwalejin. [3] Hakan ya haifar da yaye daliban ilimin likitanci na farko a Najeriya.

Digirin farko

[gyara sashe | gyara masomin]
Asibitin Jami'ar birnin Ibadan

Tsarin ilimin llikitanci na farko a Najeriya yana ɗaukar akalla shekaru shida a Jami'a kafin a yaye ɗalibai. Shekara ta farko an yi amfani da ita a Sashen Kimiyya suna karantar da su musamman a kwasa-kwasan Physics, Chemistry da Zoology, da wasu sauran darussa na gaba-ɗaya (general subjects). Tsarin shekarun da ɗalibai ke samun horo kafin fara ayyukan asibiti na ɗaukar kusan watanni 18 bayan sun haɗa da laccoci na aji da aikin gwaje-gwaje na kusan awa 9 kowace rana da ƙarin basu lokaci don nazarin karatun daga su kansu ɗaliban. Kwasa-kwasan da ake koyarwa duka tilas ne, sun haɗa da Anatomy, Physiology, Biochemistry. Samun nasara cin jarrabawar ƙwararru ke bayar da damar ci gaba da zuwa ɗaukar horo a ayyukan asibiti ga daliban da sukai ci jarabawar. Ana shafe shekaru uku da rabi ana koyar da ɗalibai a asibitin koyarwa. Darussan da ake karantarwa sun haɗa da Pharmacology, Pathology, wanda koyawar ta dogara ne a dakin gwaje-gwaje haka-zalika har zuwa shekara ta huɗu na koyar da darussan.

Shekaru biyu na ƙarshe na makarantar likitanci ana shafe su a fannin ilimin kimiyyar asibiti. Duk ƙa'idojin abubuwan da aka koyar na shekarun da suka gabata ana amfani da su ga kula da marasa lafiya ƴan adam. Likitancin fannukan Paediatrics, Ciwon ciki da Gynaecology, Magungunan Al'umma, Tiyata, Magunguna duka ana koyar da su daga wannan matakin. Bayan samun nasarar da aka yi a jarrabawar ƙarshe ta Ƙwararrun Makarantar Likita, dalibi ko dalibai zai sami Lasisi na wucin gadi don yin aikin likita a ƙarƙashin kulawa na shekara guda a Najeriya ta hannun ƙungiyar MDCN. Amincewa da makarantun likitanci da likitan hakori a Najeriya da mafi karancin ma'aunin horarwa aiki ne na hadin gwiwa na Hukumar Kula da Jami'o'i ta kasa (NUC) da kungiyar likitoci da hakori ta Najeriya (MDCN).1 A halin yanzu, a Najeriya, akwai makarantun likitanci guda 42, daga ciki; 17 na Tarayya ne, 18 kuma cibiyoyin Jiha ne, bakwai kuma na masu zaman kansu ne.

Digiri na biyu

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. Malu, A (2010). "Universities and medical education in Nigeria". Nigerian Medical Journal (51): 84–8.
  2. Malu, A (2010). "Universities and medical education in Nigeria". Nigerian Medical Journal (51): 84–8.
  3. Malu, A (2010). "Universities and medical education in Nigeria". Nigerian Medical Journal (51): 84–8.