Irène Esambo
26 ga Afirilu, 2021 -
6 Satumba 2019 - 26 ga Afirilu, 2021 | |||||
| Rayuwa | |||||
| Haihuwa | Satumba 1984 (41 shekaru) | ||||
| ƙasa | Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango | ||||
| Karatu | |||||
| Harsuna | Faransanci | ||||
| Sana'a | |||||
| Sana'a |
ɗan siyasa da human rights lawyer (en) | ||||
Irène Esambo Diata lauya ce mai kare hakkin ɗan adam kuma 'yar siyasa a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo. Mace mai naƙasa, a shekarar 2019 Esambo ta zama ministar mutanen da ke da naƙasa ta farko a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo. [1] A gwamnatin Lukonde ta shekarar 2021 ta ci gaba da riƙe muƙaminta a majalisar ministoci, a matsayin minista mai wakiltar Ministan Harkokin Jama'a, mai kula da Naƙasassu da Sauran Mutane Masu Rauni.[2]
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Irène Esambo ta shafe shekaru da yawa tana aikin lauya a Kinshasa, tare da ƙwarewa a shari'o'in cin zarafin mata, haƙƙin naƙasassu da kuma waɗanda yaƙi ya shafa. Ta kasance shugabar Cibiyar Shari'a da Résolution 1325 (CJR), tana da niyyar yin garambawul ga ɓangaren tsaro bisa ga ƙudurin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya mai lamba 1325. A shekarar 2013 an naɗa ta a matsayin lauya a Kotun Laifuka ta Duniya. [3]
A watan Agusta na shekarar 2019, an sanar da Esambo a matsayin memba na gwamnatin Ilunga, inda ta karɓi sabon muƙamin Wakilci ga Ministan Harkokin Jama'a don kula da mutanen da ke fama da naƙasa da sauran marasa galihu.[4]
A shekarar 2020 ta yi aiki don shirya dokar kare hakkin naƙasassu ga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. [1]
Bayan watanni da dama na tattaunawa kan tsarin sabuwar gwamnati, an sanar da gwamnatin Lukonde a ranar 12 ga watan Afrilu 2021.[1] Esambo ta ci gaba da zama ministar da ke wakiltar naƙasassu a cikin sabuwar majalisar ministoci. [5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 2 3 Karolina Kozik; Jean-Sébastien Sépulchre (11 March 2020). "Disability Rights Bill Offers Hope in Congo". Human Rights Watch. Archived from the original on 2022-02-13. Retrieved 11 February 2022. Cite error: Invalid
<ref>tag; name "HRW" defined multiple times with different content - ↑ The International Directory of Government 2021. Europa Publications. 2021. pp. 475–476. ISBN 9781000521375.
- ↑ "Female lawyer from the Democratic Republic of Congo appointed at the International Criminal Court". Cordaid. 7 May 2013. Archived from the original on 2022-02-13. Retrieved 11 February 2022.
- ↑ "La RDC enfin dotée du Gouvernement de l'alternance démocratique". Digital Congo. 26 August 2019. Archived from the original on 2022-02-13. Retrieved 11 February 2022.
- ↑ Romain Gras; Stanis Bujakera Tshiamala (14 April 2021). "DRC: President Tshisekedi finally forms a government". The Africa Report. Archived from the original on 2022-02-13. Retrieved 11 February 2022.