Isa Mustapha Agwai I Polytechnic
| Bayanai | |
|---|---|
| Iri | makaranta |
| Ƙasa | Najeriya |
Isa Mustapha Agwai I Polytechnic (IMAP) kwalejin kimiyya da fasaha ce ta jiha a Laiya, Jihar Nasarawa, Najeriya. An kafa ta a ranar 15 ga watan Agustan shekara ta 2000 a matsayin makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Nasarawa, Lafiya, tsohon gwamnan Nassarawa Abdullahi Adamu, shine wanda ya kafa makarantar. Dokta Nuruddeen Mu'azu Maifata shine shugaban makarantar na yanzu.[1]
A shekarar 2019, an sauya sunan makarantar don girmama marigayi Sarkin Lafia, Alhaji Isa Mustapha Agwai I (1935-2019). Babban filin makarantar yana kusa da Jos Road, kimanin kilomita 5 daga garin Lafia.
Akadamiyya
[gyara sashe | gyara masomin]Makarantar ta ƙunshi tsangayu biyar: Nazarin Kasuwanci da Gudanarwa, Kimiyya mai amfani, Fasahar Injiniya, Nazarin Muhalli, da Nazarin Gaba ɗaya.
Ɗakin karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai Laburare a makarantar, wanda aka kafa a shekara ta 2001, ya ƙunshi littattafai sama da 30,000 da kuma e-library tare da kayan aikin ICT.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Johnson, Chris (2 July 2025). "NewsNasarawa: Governor Sule appoints Maifata as substantive rector of IMAP". dailypost.ng. Retrieved 9 November 2025.