Isah Misau
6 ga Yuni, 2015 - District: Bauchi Central | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | 1970 (55/56 shekaru) | ||
| Karatu | |||
| Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress | ||
Hamma Isah Misau (an haife shi 1970 a Jihar Bauchi, Najeriya) ɗan siyasar Najeriya ne. Tsohon sanata daga Bauchi ta tsakiya shine tsohon shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan Navy na Najeriya. [1][2]
Misau yayi karatu a babbar Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, Kaduna inda yayi karatu kuma ya samu digiri a harkar Kasuwanci a 1997. A shekara ta 2010, ya samu digiri na biyu a fannin aikin lauya daga Jami’ar Ahmadu Bello.
Isah Misau ya fara aikinsa ne a shekarar 2000 a matsayin jami'in Gudanarwa a rundunar 'yan sanda ta Nijeriya sannan ya yi aiki a rundunar har tsawon shekaru goma kafin ya yi murabus. A shekarar 2015, Misau ya bayyana aniyarsa ta neman takarar kujerar sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya sannan ya lashe zaben a watan Maris din 2015, inda ya kayar da tsohon Mataimakin Shugaban masu rinjaye Abdul Ningi. [3][4][5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "National Assembly is supreme, they should respect us - Sen. Isah Misau - Vanguard News". Vanguardngr.com. Retrieved 2020-01-08.
- ↑ "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". Nass.gov.ng. Retrieved 2020-01-08.
- ↑ http://dailypost.ng/2015/03/31/senate-leader-defeated-in-bauchi-as-saraki-wins-in-kwara/
- ↑ 6:17 pm (2015-09-29). "Full list of 83 senators who passed vote of confidence on Saraki - Vanguard News". Vanguardngr.com. Retrieved 2020-01-08.
- ↑ "Angry Youths Attack Pro-Saraki Senator Isah Misau In Bauchi". Sahara Reporters. 2016-04-18. Retrieved 2020-01-08.