Jump to content

Isatou Njie-Saidy

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Isatou Njie-Saidy (wanda kuma aka rubuta Aisatu N'Jie-Saidy; an haife ta a ranar 5 ga watan Maris 1952) 'yar siyasan Gambiya ce. Ta kasance mataimakiyar shugabar ƙasar Gambiya, da kuma sakatariyar harkokin mata, daga ranar 20 ga watan Maris 1997 zuwa 18 ga watan Janairu 2017. Ita ce mace ta farko 'yar Gambia da ta taɓa riƙe muƙamin mataimakiyar shugaban ƙasa kuma ɗaya daga cikin mata na farko a siyasar yammacin Afirka da suka kai wannan babban matsayi. [1]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Njie-Saidy a Kuntaya a ranar 15 ga watan Maris, 1952 sashin Bankin Arewa. Daga shekarun 1959 zuwa 1964, ta halarci Makarantar Firamare ta Brikama, kuma daga shekarun 1964 zuwa 1970, ta yi karatu a Makarantar Sakandare ta Armitage, Georgetown. A shekarar 1971, ta halarci Kwalejin Horar da Malamai ta Yundum, inda ta samu gurbin zama malama a shekarar 1974. Daga watan Yuli 1979 zuwa Disamba 1979, ta yi karatu a Cibiyar Nazarin Kimiyyar Gudanarwa, Jami'ar Fasaha ta Delft, a Netherlands, inda aka ba ta takardar shaidar digiri na biyu a fannin sarrafa masana'antu. Daga watan Satumba zuwa Nuwamba 1981, ta yi karatu a Jami'ar Philippines, inda ta sami takardar shaida a kan small-scale industrial information management. A cikin watan Satumba 1988, ta kammala Masters of Science in Social and Economic Development a Jami'ar Swansea. [1]

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Daga watan Satumba 1983 zuwa Disamba 1989, Njie-Saidy ta kasance mataimakiyar Sakatariyar Zartarwa ta Ofishin Mata, kwamitin zartarwa na Majalisar Mata ta Ƙasa.[2][3] Shekaru biyu bayan juyin mulkin 1994 na Gambia inda Yahya Jammeh ya kwace mulki, a watan Yulin 1996 Njie-Saidy aka naɗa a matsayin ministar lafiya, jin daɗin jama'a da harkokin mata. A ranar 20 ga watan Maris, 1997 'yan watanni bayan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 1996 wanda ya lashe zaɓen shugaba Jammeh, an naɗa Njie-Saidy a matsayin mataimakiyar shugaban ƙasar Gambia da sakatariyar harkokin lafiya, jin daɗin jama'a da harkokin mata. [1]

Ta yi magana kuma ta yi rubuce-rubuce da yawa game da batutuwan mata a Gambia.[4][5]

A watan Disambar 2015, dangantakar Njie-Saidy da Jammeh ta yi tsami. A cewar jaridar Freedom Newspaper, wani makusancin Jammeh ya ruwaito cewa "Jammeh ya sanar da su cewa ba ya son ganin Isatou Njie Saidy. Ya bayyana Isatou a matsayin "mugun mutum" wanda ya taimaka wajen gazawar gwamnatinsa. Jammeh ya shaida wa mukarrabansa cewa zai maye gurbin Isatou Njie Saidy."[6]

A ranar 18 ga watan Janairu 2017, Njie-Saidy ta yi murabus a tsakiyar rikicin tsarin mulkin 2016-17, tare da wasu ministocin gwamnati da dama. [7]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Njie-Saidy tana da aure kuma tana da ‘ya’ya huɗu. Tana jin harsuna da dama, wato: Mandinka, Fulani, Wolof, Turanci da Faransanci.

  1. 1.0 1.1 1.2 "Office of The Vice President of Gambia". Access Gambia. Retrieved 19 June 2016. Cite error: Invalid <ref> tag; name "acgam" defined multiple times with different content
  2. "H.E. Isatou Njie Saidy launches National Policy for Advancement of Gambian Women". Archived from the original on 2 March 2007. Retrieved 9 July 2017.
  3. "Office of the President: Gambia: State House". Archived from the original on 5 February 2008. Retrieved 28 December 2016.
  4. "H.E. Isatou Njie Saidy launches National Policy for Advancement of Gambian Women". Archived from the original on 2 March 2007. Retrieved 9 July 2017.
  5. "Office of the President: Gambia: State House". Archived from the original on 5 February 2008. Retrieved 28 December 2016.
  6. "Gambia: Jammeh To Fire His Vice President Isatou Njie Soon!". Freedom Newspaper. 9 December 2015. Archived from the original on December 14, 2015. Retrieved 19 June 2016.CS1 maint: unfit url (link)
  7. AfricaNews (18 January 2017). "Gambia's Vice President resigns hours before Jammeh's mandate ends". Africanews. Retrieved 9 July 2017.