Isyaka Rabi'u

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u malamin addinin musulunci ne, kuma shahararren dan kasuwa ne wanda ya dade yana ayyukan taimakawa al'umma a lokacin rayuwarsa.

Tarihin sa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifi marigayi Isyaku Rabi'u a 1928 ga iyalan Muhammadu Rabi'u Dan Tinki, wanda mai wa'azin addinin musulunci ne daga Bichi cikin jihar Kano a Najeriya.

Daga 1936 zuwa 1942, marigayin ya halarci makarantar allo ta mahaifinsa, inda aka horar da shi kan Alkur'ani da Larabci.


Daga nan ya tafi Maiduguri domin karo ilimi, kuma bayan ya gama karatunsa a can ne ya dawo gida da niyyar yin aure.

Bayan ya yi auren kuma ya tafi Zaria gidan wani shahararran Malami, mai suna Malam Na'iya, inda ya samu shekaru biyu yana dalibta.

A shekarar 1949 ya kasance malamin addini mai zaman kansa, inda yake koyar da Larabci da Alkur'ani ga dalibansa. Kuma a cikin daliban akwai Ibrahim Musa Gashash.

A farko shekarun 1950 Mallam Isyaku Rabi'u ya fara kasuwanci, duk da cewa bai bar koyarwa ba. Ya kafa wani kamfani mai suna Isyaku Rabiu & Sons a 1952.

Da farko kamfanin ya fara da zama dilan kayan kamfanin UAC ne, wanda a wancan lokacin ke kasuwanci akan kekunan dinki, da litattafan addinin Musulunci da kuma kekuna.

A 1958, kamfanin ya sami bunkasa bayan da aka kafa masakar Kaduna Textile Limited kuma kamfanin na Isyaku Rabiu & Sons ya zama daya daga cikin dilolinsa na farko.

Marigayin ya zama babban dilan kamfanin a arewacin Najeriya, kuma a 1963 shi da wasu 'yan kasuwa daga Kano suka hadu don kafa Kano Merchants Trading Company.

Wannan kamfanin ya jure wa gasa daga kamfanonin da ke shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Ya kuma kafa wani kamfani mai dinka kayan sawa a 1970.

A lokacin da aka fara siyasar janmuriya ta biyu, marigayi Sheikh Isyaku Rabi'u ya goyi bayan jam'iyyar NPN wadda ta mulki kasar.

Kasuwanci[gyara sashe | Gyara masomin]

Kamfanin da marigayin ya kafa na Isyaku Rabiu & Sons a matsayin kamfani mai kasuwancin gine-gine da harkar inshora da na banki da kuma saye da sayarwar filaye.

A shekarun 1970, kamfanin ya zuba jari cikin harkar hada akwatuna da jakukkuna, kuma wannan wani hadin gwuiwa ne da wasu masu zuba jari daga Lebanon.

A 1972 ya kafa masakar Bagauda Textile Mill, masu saka zannuwa da kayan inifom, inda daga nan ne ya kafa wasu kamfanonin da ke kasuwanci a bangarori daban-daban na tattalin arzikin kasar.

Wasu daga cikin sassan sun hada da kasuwanci kan kifi, da harkar gidaje da filaye, da siga, da kamfanin da ke samar da kayan motoci musamman na Daihatsu.

Amma saboda faduwar darajar Naira, kamfanin ya mayar da hankalinsa wajen kere-kere da kasuwanci kaya.

Iyalan sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Marigayi Isyaku Rabi'u ya rasu ya bar mata da 'ya'ya har da jikoki masu yawa, kuma a cikin 'ya'yansa akwai Nafiu Rabiu, wanda shi ne babban dansa. Akwai kuma babban dan kasuwan nan, Abdulsamad Rabiu, wanda shi ne shugaban kamfanonin BUA.

Akwai kuma Rabi'u Rabi'u, mai kamfanin jirgin sama na IRS Airlines, da Naziru Rabi'u, da Quraish I Rabi'u, da Makiu Rabi'u, sai Abdullahi Rabi'u, da Muhammad Rabi'u, da Daha Rabi'u.

Kuma a fili yake cewa gidan marigayin na cikin gidaje mafi girma a duk fadin Kano.

Ayyukan sa domin taimaka ma al'uma[gyara sashe | Gyara masomin]

Ban da fagen karatun addini da kaswanci, marigayi Sheikh Isyaku Rabi'u ya yi fice wajen ayyukan taimako, wanda ya sa mutane da dama ke kaunarsa.

Malam Isyaka Rabi'u sanannen dan darikar Taijjaniyya ne, kuma yana daya daga cikin manyan almajiran shiek Ibrahim Nyass Kaulaha.

Madogara[gyara sashe | Gyara masomin]