Jump to content

Jamaluddin Hossain

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jamaluddin Hossain
Rayuwa
Haihuwa 14 Oktoba 1943
ƙasa Bangladash
Mutuwa Rockyview General Hospital (en) Fassara, 11 Oktoba 2024
Karatu
Makaranta Bangladesh University of Engineering and Technology (en) Fassara
Harsuna Bangla
Sana'a
Sana'a jarumi, darakta da dan wasan kwaikwayon talabijin
Kyaututtuka
IMDb nm8867511

Jamaluddin Hossain (an haife shi a ranar 8 ga Oktoban shekara ta 1943 -Ya mutu a ranar 11 ga Watan Oktoban shekarar 2024) ya kasance ɗan wasan kwaikwayo na ƙasar Bangladesh, darektan kuma mai fafutukar wasan kwaikwayo. Gwamnatin Bangladesh ta ba shi lambar yabo ta Ekushey Padak a shekarar 2013..[1][2]

Ilimi da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Hossain a ranar 14 ga Oktoban shekarar 1943 a cikin 24 Parganas a Lardin Bengal na lokacin, Indiya ta Burtaniya. Bayan rabuwa da Indiya a shekarar 1947, iyalinsa sun zauna a Chittagong a Gabashin Bengal a lokacin.[3] Ya fara karatu a Makarantar Saint Placid a Chittagong. [3] Daga nan ya kammala karatu daga Kwalejin Chittagong da Jami'ar Injiniya da Fasaha ta Bangladesh. Ya kasance abokin aji na ɗan wasan kwaikwayo Abul Hayat a cikin waɗannan cibiyoyin.[4][5]

Hossain ya kasance memba na Nagarik Natya Sampradaya, ƙungiyar wasan kwaikwayo daga Shekarar 1975 har zuwa shekara ta 1995. A shekara ta 1997, ya fara ƙungiyarsa ta Nagarik Natyangan Ensamble kuma ya yi aiki a matsayin babban sakatarenta. Ya kasance memba na presidium na Ƙungiyar Wasanni ta ƙasar Bangladesh (BGTF) kuma babban sakatare na Betar Television Shilpi Sangsad.

Rayuwa da mutuwarsa

[gyara sashe | gyara masomin]

Hossain ya auri ƴar wasan kwaikwayo Rowshan Ara Hussain a shekarar 1965. Sun haɗu yayin da suke mambobin ƙungiyar wasan kwaikwayo ta Nagarik Natya Sampradaya . Ɗansu, Tasfin Hossain Topu, mataimakin farfesa ne a Jami'ar Mount Royal da ke ƙasar Calgary .

Hossain yana cikin magani a Babban Asibitin Rockyview a ƙasar Calgary lokacin da ya mutu a ranar 11 ga Oktoban shekarar 2024, yana da shekaru 81.

Hossain ya ba da umarnin shahararrun wasan kwaikwayo ciki har da Khanchar Bhitor Achin Pakhi, Raja Rani, Chand Boniker Pala, Ami Noi, Bibishab da Jugol Bondi.[6][7][8][1][9][10]

  1. 1.0 1.1 "Nagorik Natyangan Ensemble goes to Kolkata". The Daily Star (in Turanci). 2010-04-24. Retrieved 2018-01-06.
  2. একুশে পদকপ্রাপ্ত সুধীবৃন্দ [Ekushey Padak winners list] (in Bengali). Government of Bangladesh. Retrieved 23 August 2017.
  3. 3.0 3.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named kemon
  4. "Theatre as an indispensable part of existence". The Daily Star (in Turanci). 2013-03-06. Retrieved 2018-01-06.
  5. "Dhaka: Yesterday, today and tomorrow". The Daily Star. 2006-08-07. Archived from the original on 2018-01-06. Retrieved 2018-01-06.
  6. "Nagorik Natyangan Ensemble's upcoming production : Khanchar Bhitor Achin Pakhi". The Daily Star. 2006-07-26. Archived from the original on 2018-01-06. Retrieved 2018-01-06.
  7. "Three New Plays Staged Over the Weekend". The Daily Star (in Turanci). 2011-02-06. Retrieved 2018-01-06.
  8. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named strive
  9. "Theatre festival by Nagarik Natyangan Ensemble ends". The Daily Star (in Turanci). 2013-01-05. Retrieved 2018-01-06.
  10. "Theatre festival to pay homage to Kalim Sharafi". The Daily Star (in Turanci). 2012-12-30. Retrieved 2018-01-06.

Hanyoyin Haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]