Jump to content

Jamila Hussain

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jamila Hussain
Rayuwa
Haihuwa 1942
Mutuwa 2016
Sana'a
Sana'a Malami

Jamila Hussain (1942, Katoomba - 31 ga watan Agusta 2016, Sydney ) shugabar al'ummar Musulmi ce na ƙasar Ostiraliya kuma malamar jami'a a Jami'ar Fasaha ta Sydney .

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife ta a shekarar 1942 a Katoomba, New South Wales, kuma ta yi karatu a Jami'ar Sydney. Ta auri wani mutum Musulmi ɗan China kuma ta yi karatun Shari'a a Malaysia. Mijin ta ya rasu a shekarar 1994, ta koma Ostiraliya ta ci gaba da aiki a matsayin shugabar al'umma, mai sharhi, kuma malama. [1] Ita ce mawallafiyar littafin Islam, its law and Society. [2] [3] Ta rasu a shekarar 2016. Sharhinta na bainar jama'a game da addinin Musulunci, Shari'a da matsayinta a Ostiraliya ya bayyana a jaridar Sydney Morning Herald, [4] [5] SBS [6] da kuma a cikin tattaunawa da gidan talabijin na ABC . [2]

  1. Media, AMUST (September 25, 2016). "Jamila Hussain, an Australian Muslim Pioneer".
  2. 1 2 "Second Hour: Jamila Hussain :: Sunday Nights". www.abc.net.au.
  3. "Dr Jamila Hussain". ABC Radio National. October 15, 2009.
  4. Hussain, Jamila (September 23, 2014). "Sharia 101: a user's guide for Jacqui Lambie". The Sydney Morning Herald.
  5. Hussain, Jamila (November 24, 2008). "Islam at a cultural crossroad". The Sydney Morning Herald.
  6. "What is Sharia law?". News. Archived from the original on 22 October 2021. Retrieved 14 July 2021.