Jump to content

Jean Bernadt

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jean Bernadt
Rayuwa
Haihuwa 19 Mayu 1914
ƙasa Afirka ta kudu
Mutuwa 9 ga Afirilu, 2011
Sana'a
Sana'a anti-apartheid activist (en) Fassara

Jean Bernadt (née Alkin) (19 Mayu 1914 - 9 Afrilu 2011) 'yar gwagwarmayar yaƙi da wariyar launin fata ce ta Afirka ta Kudu. [1]

Ta kasance memba mai ƙwazo a Jam'iyyar Kwaminis ta Afirka ta Kudu (CPSA), Congress of Democrats, Ƙungiyar Mata ta Afirka ta Kudu da Black Sash a tsakanin sauran cibiyoyi. A shekarar 1940 ta auri Himan (Himie) Bernadt kuma ta haifi 'ya'ya uku.

A shekarar 1934 tayi karatu a High School Cape Town [2]

A shekarar 1936 tayi karatu a Jami'ar New York - tayi nazarin Adabin Amurka [2]

Ta kasance cikin ƙungiyoyin agaji da yawa, yawanci tare da wasu mata daga Black Sash da Jam'iyyar Kwaminisanci. Ta kasance memba na Kwamitin Athlone don Ilimin Nursery. Kwamitin Athlone ya kafa makarantar reno na farko don yara masu launi a Athlone a cikin shekarar 1949 sannan kuma ta kafa gidan wasan kwaikwayo na Open-Air na Maynardville a ranar 1 ga watan Disamba 1950 a matsayin mai tara kuɗaɗe na agaji ga yankunan marasa galihu. Ita da Margaret Molteno (shugaban kuma wanda ya kafa kwamitin Athlone) sun haɗu tare da shugabar al'ummar Blouvlei Dora Tamana a cikin shekarar 1954 don yin aiki kan ayyukan al'umma a cikin Blouvlei na yau da kullum. Tun a shekarar 1948, Tamana ta fara aikin al'umma a wani gida mai zaman kansa, amma ya tsaya bayan shekara biyu da rabi saboda rashin kuɗi. Matan ukun sun tattara kuɗaɗe kuma suka kafa makarantar Nursery Blouvlei da cibiyar kula da lafiyar iyali bisa ga tsare-tsaren Tamana a watan Mayu 1955.[3]

Ta kasance ƙarƙashin dokar hana gwamnati daga shekarun 1959 zuwa 1964. Daga baya ta ajiye Nelson Mandela a lokacin da yake tattaunawa da gwamnatin nuna wariyar launin fata. [4] A shekarar 1960 aka kama ta kuma ta yi watanni uku a gidan yari. [5]

Bikin Tunawa

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 2008, Jean Bernadt da mijinta an yi bikin tunawa da su kuma an ba su lambar yabo ta Luthuli a azurfa saboda adawa da nuna wariyar launin fata da kuma kare masu fafutukar yaki da nuna wariyar launin fata.[6]

  1. "Black Sash - Making Human Rights Real - in memory of Jean Bernadt". Archived from the original on 2017-08-10. Retrieved 2017-08-10.
  2. 2.0 2.1 "Jean Bernadt (nee Alkin) | South African History Online". www.sahistory.org.za. Retrieved 2020-06-15. Cite error: Invalid <ref> tag; name "SAHO" defined multiple times with different content
  3. Tasmin Cupido: Peoples Post Retreat. Cape Town. 1 May 2014. p.3. Blouvlei Nursery: Mandela-sponsored Revamp Rejuvenates 60 year old creche.
  4. Leander (2012-11-29). "Jean Bernadt (nee Alkin)". South African History Online (in Turanci). Retrieved 2019-04-02.
  5. "Farewell to an icon who spent her life fighting apartheid". 5 May 2011. Retrieved 2020-06-15 – via PressReader.
  6. Guardian Staff (2017-09-30). "Family life: My mother in Cape Town before her arrest; Bless This House; ice-cream pudding". The Guardian (in Turanci). ISSN 0261-3077. Retrieved 2020-06-15.