Jump to content

Jemage

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jemage
Scientific classification
SubkingdomBilateria (en) Bilateria
PhylumChordata
Classmammal (en) Mammalia
SuperorderLaurasiatheria (en) Laurasiatheria
order (en) Fassara Chiroptera
Blumenbach, 1779
Geographic distribution
General information
Tsatso bat meat (en) Fassara
Tsawo 6 ft da 1 in
Audible frequency range 2,000 hertz (en) Fassara — 110,000 hertz (en) Fassara
jemage maƙale akan bishiya
jemage yana fira
jemagu akan bishiya
jemagu da yawa akan bishiya
jemagen sirilanka akan hannu
jemagu suna tashi a sama
dayigiram ɗin jemagu
jemagun indiya

Jemage halitta ce dake a cikin nau'ukan halitta na mammals, wasu na zacin jemage amatsayin tsuntsu, amma ba'a dangin tsuntsaye yake ba. Jemage na daya daga cikin dabbobi masu shayarwa na tsarin Chiroptera (/kaɪˈrɒptərə/).[1] suna amfani da ƙwaƙƙwaran gabansu, wato gabobin su na farko a matsayin fuka-fuki, su ne kawai dabbobi masu shayarwa waɗanda ke shawagi mai dorewa. Jemage sun fi saurin tashi sama fiye da yawancin tsuntsaye, suna tashi da yatsun su masu tsayi da yalwa wanda suke lulluɓe da siraran nama.

Jemagu sun kasance a tsari na biyu mafi girma na dabbobi masu shayarwa bayan Beraye, sun kuma ƙunshi kusan kashi 20% na dukkan nau'ikan dabbobi masu shayarwa a duniya, fiye da nau'ikan 1,400. An raba waɗannan a gargajiyance zuwa gida biyu: Manyan-jemage (megabats) masu cin 'ya'yan itace da masu amfani da amsawar sauti domin gane inda abu yake wato Kananun-jemage (Microbats). Yawancin jemagu suna cin kwari ne, wasu kuma suna cin 'ya'yan itace ko furanni. kadan daga ciki ne suke cin wani abu daga dabbobi banda kwari; misali, jemage mai shan jini, wanda ya kasance yana tsutsar jini daga jikin dabbobi. Yawancin jemagu 'Yan-dare ne, kuma da yawa suna zama a cikin kogo ko wasu mafaka; Babu tabbas ko jemagu suna da waɗannan halayen domin tsira daga mafarauta. Jemage suna nan a duk faɗin duniya, ban da yankuna masu tsananin sanyi.


Amfanin Jemage

[gyara sashe | gyara masomin]

Jemage suna ba wa ɗan adam wasu fa'idodi kai tsaye, a farashin wasu rashin amfani. An haƙa kashin jemagu daga kogo kuma an yi amfani dashi azaman taki. Jemagu suna da muhimmanci a wurin auratayya tsakanin furanni da kuma yad'a iri; inda da yawa shuke-shuken da ke cikin Hamada sun dogara ga jemagu domin wannan aiki. Jemage na cinye kwari, wanda hakan yana rage buƙatar magungunan kashe qwari da sauran matakan sarrafa kwari. Koyaya de, wasu jemagu suma mafarauta ne na sauro, suna hana yaduwar cututtuka da sauro ke haifarwa. Masu noman 'ya'yan itace galibi suna ɗaukar jemagu a matsayin kwari masu 'barna. Saboda halittar jikinsu, jemagu nau’in dabba ne da ke aiki a matsayin ma'adanar cututtuka masu yawa, irin su ciwon Rabies; inda suke samun damar hakan, kasancewar suna da tafiye-tafiye, huld'ayya, da kuma tsawon rai, za su iya yada cuta a tsakanin junansu da sauri, huldar mutane da jemagu zata iya kasancewa mai hadari.


Ya danganta da al'ada, ana iya alakanta jemagu da abubuwa masu kyau, kamar kariya daga wasu cututtuka ko haɗari, sake haifuwa, ko tsawon rai, amma a yammaci, ana alakanta jemagu da duhu, lalata, maita, yan shan jini, da mutuwa.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


  1. "Chiroptera" . Encyclopædia Britannica. Vol. 6 (11th ed.). 1911. pp. 239–247.