Lagos (jiha)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Jihar Legas)
Lagos


Suna saboda Lagos
Wuri
Map
 6°35′N 3°45′E / 6.58°N 3.75°E / 6.58; 3.75
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Ikeja
Yawan mutane
Faɗi 11,000,598 (2016)
• Yawan mutane 3,075.37 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 3,577 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Tekun Guinea da Lagos Lagoon
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Western Region (en) Fassara
Ƙirƙira 27 Mayu 1967
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Majalisar Zartaswa ta Jihar Legas
Gangar majalisa Lagos State House of Assembly
• Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu (29 Mayu 2019)
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-LA
Wasu abun

Yanar gizo lagosstate.gov.ng
Jihar lagos
Cikin Birnin Lagos

Jihar Lagos jiha ce da ke Kudu maso Yammacin Najeriya. Acikin duka jihohin Najeriya, itace jiha mai mafi yawan jama'a kuma itace mafi ƙanƙanta ta fuskar girma. Ta haɗa iyaka da daga kudu da Bight of Benin, daga yamma kuwa da iyaka na kasa da kasa da Jimhurriyar Benin, Jihar Legas ta haɗa iyaka da Jihar Osun daga gabas da kuma yamma wanda hakan ya sanya ta zamo jiha kaɗai da ta haɗa iyaka da wata jiha daga ɓangarori guda biyu. Ta samo sunanta daga babban birnin ta na Legas, wanda itace birni mafi girma ta fuskar yawan jama'a a Afirka. Jihar ta samo asali ne daga Jihar Yammacin Najeriya kuma tsohuwar Babban Birnin Najeriya a ranar 27 ga watan Mayun 1967.

Ta fuskar yanayin ƙasa, Jihar mamaye take da ruwaye waɗanda suka mamaye aƙalla kaso uku cikin huɗu na faɗin jihar wanda suka haɗa suka haɗa da ta kuna, creek da kuma koguna. Mafi girmansu sune tafkin lagoon dake Legas da kuma Lekki a yankin cikin garin inda ruwa daga kogin Osun da na Ogun ke kwararar a cikinsu. Ƙoramu da tafkuna da dama na kwarara a cikin garin kuma suna cikin muhimman hanyoyin sufuri na mutane da kaya a jihar. Akan ƙasa kuwa, akwai Ƙauyuka da dama a yankunan ƙarin jihar waɗanda ke da dabbobi da suka fara Ƙwarewa kaman birrai nau'in Mona, tree pangolin, angulu da sauran tsirarun nau'ikan giwayen Afirka a dazukan. Acikin ruwa kuwa akwai dabbobi iri-iri waɗanda suka haɗa da dabbar African manatee da kadoji.

Ƙabilu da dama ne ke zaune a Jihar Legas na tsawon shekaru tare da Ƙabilar Yarbawa a matsayin asalin mazauna garin waɗanda ke zaune a ko ina a faɗin jihar tare da mutanen Ewe da Mutanen Ogu daga can ƙuryar yammacin jihar. A dalilin hijira da ya wanzu tun a karni na 19, mutane iri iri 'yan asalin Najeriya da ƙasa hen kewaye ke zaune a yankin kamar Mutanen Edo, Fulani, Hausawa, Igbo, Mutanen Ijaw, Mutanen Ibibio da Nufawa da dai sauransu. Har wayau akwai ƙabilu daga ƙasashen wajen Najeriya ta yau wnda suka haɗa da Saro (Mutanen Ƙasar Sierra Leone) da kuma Amaro (Mutanen Brazil) da ke zaune a Najeriya waɗanda iyalai ne na bayi da suka dawo Afirka a ƙarni na 1800. Tare da sauran 'Yan gudun hijira na kwanannan daga yankunan Ƙasashen Sin, Ghana, Indiya, Togo da kuma Birtaniya waɗanda ke taka muhimmin rawa a ɓangaren bunƙasar yawan mutanen jihar. Ta fuskar addinai kuwa, Jihar ta rarrabu tsakanin kaso 55% a matsayin kiristoci, musulmai kuma Kusan kimanin kaso 40%, da kuma kaso 5% waɗanda ke bin a Dinan gargajiya ko wani hakan.

Tana da yawan fili kimani na kilomita araba’in3,577 da yawan jama’a miliyan sha bakwai da dubu ɗari biyar da hamsin da biyu da ɗari tara da arba'in (jimillar 2012). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Legas. Babajide Sanwo-Olu, shi ne gwamnan jihar tun zaɓen shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Oluranti Adebule. Dattijai a jihar sun haɗa da: Bola Tinubu, Oluremi Tinubu, Solomon Olamilekan Adeola da Gbenga Bareehu Ashafa.

Kasuwar kayan miya a lagos

Ƙananan Hukumomi[gyara sashe | gyara masomin]

Lagos

Jihar Lagos ta rabu gida Biyar (5) wurin rabe-raben ayyuka, waɗanda suka ƙara rabuwa zuwa ƙananan Hukumomi ashirin (20). Sune:[1]

Sunan Karamar hukuma Fadin kasa (km2) Kidayar Jama'a
ta 2006
Cibiyar Karamar hukuma Lambar
Aika Sako
Agege 11 459,939 Agege 100
Alimosho 185 1,277,714 Ikotun 100
Ifako-Ijaye 27 427,878 Ifako 100
Ikeja 46 313,196 Ikeja 100
Kosofe 81 665,393 Kosofe 100
Mushin 17 633,009 Mushin 100
Oshodi-Isolo 45 621,509 Oshodi/Isolo 100
Shomolu 12 402,673 Shomolu 101
Ikeja Division 424 4,801,311
Apapa 27 217,362 Apapa 101
Eti-Osa 192 287,785 Ikoyi 101
Lagos Island 9 209,437 Lagos Island 101
Lagos Mainland 19 317,720 Lagos Mainland 101
Surulere 23 503,975 Surulere 101
Lagos Division 270 1,542,279
Ajeromi-Ifelodun 12 684,105 Ajeromi/Ifelodun 102
Amuwo-Odofin 135 318,166 Festac Town 102
Ojo 158 598,071 Ojo 102
Badagry 441 241,093 Badagry 103
Badagry Division 746 1,841,435
Ikorodu 394 535,619 Ikorodu 104
Ikorodu Division 394 535,619
Ibeju-Lekki 455 117,481 Akodo 105
Epe 1,185 181,409 Epe 106
Epe Division 1,640 298,890
Total 3,474 9,019,534 Ikeja

Sha shidan (16) farko na sunayen dake sama, sun ƙunshi wurare ne daga cikin garin birnin Lagos. Sauran Ƙananan hukumomi huɗun (4) kuma, wato (Badagry, Ikorodu, Ibeju-Lekki ds Epe) suna daga Jihar ne, amma ba daga cikin garin Birnin Lagos ba.

A shekara ta 2003, yawancin Ƙananan hukumomi ashirin (20) dake nan a yanzu, an rarraba su domin harkokin gudanar da aiki zuwa Local Council Development Areas. Waɗanda sune a yanzu suka kai adadi 56, sune: Agbado/Oke-Odo, Agboyi/Ketu, Agege, Ajeromi, Alimosho, Apapa, Apapa-Iganmu, Ayobo/Ipaja, Badagry West, Badagry, Bariga, Coker Aguda, Egbe Idimu, Ejigbo, Epe, Eredo, Eti Osa East, Eti Osa West, Iba, Isolo, Imota, Ikoyi, Ibeju, Ifako-Ijaiye, Ifelodun, Igando/Ikotun, Igbogbo/Bayeku, Ijede, Ikeja, Ikorodu North, Ikorodu West, Ikosi Ejinrin, Ikorodu, Ikorodu West, Iru/Victoria Island, Itire Ikate, Kosofe, Lagos Island West, Lagos Island East, Lagos Mainland, Lekki, Mosan/Okunola, Mushin, Odi Olowo/Ojuwoye, Ojo, Ojodu, Ojokoro, Olorunda, Onigbongbo, Oriade, Orile Agege, Oshodi, Oto-Awori, Shomolu, Surulere and Yaba.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Lagos State - Population". Archived from the original on 2011-06-15. Retrieved 2018-12-18.
  2. "Local Government Areas". Archived from the original on 2010-03-24. Retrieved 2010-03-20.


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara