Zamfara
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
|
|||||
![]() | |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Gusau | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 4,515,427 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 113.56 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 39,762 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | jihar Sokoto | ||||
Ƙirƙira | 1 Oktoba 1996 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa |
executive council of Zamfara State (en) ![]() | ||||
Gangar majalisa |
Zamfara State House of Assembly (en) ![]() | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-ZA | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | zamfarastate.net… |
Jihar Zamfara Jiha ce da take a arewa maso yammacin kasar Najeriya. Tana da yawan fili kimanin kilomita rabba’i 39,762 da yawan jama’a kimanin mutane 3,838,160 (milyan uku da dubu ɗari takwas da talatin da takwas da ɗari daya da sittin) (jimillar shekara ta 2011). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Gusau. Bello Matawalle shi ne gwamnan jihar tun hukuncin da kotu ta yanke a kan APC, shi ne ya ba shi damar zama gwamnan ta a shekara ta 2019 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Mahadi Ali Gusau. Dattijan jihar su ne: Janar Ali Gusau Ritaya,Ahmad Rufai Sani, Mamuda Aliyu Shinkafi, AbdulAziz Yari,Hassan Nasiha,Sahabi Liman Kaura, Mansur Dan'Ali,Kabir Garba Marafa, Dauda Lawal Dare, Hajiya Sadiya Umar Faruk da Tijjani Kaura.
.
Tarihin Zamfara[gyara sashe | Gyara masomin]
Asalin Zamfarawa
Zamfara ta kasance daya daga cikin masarautun asali na Hausawa. Ta kasance ana lissafata daya daga cikin Banza Bakwai wadanda ba Hausawan asali ne ba. Dalilin hakan shi ne, ana ganin Bare-Bari ne asalin Zamfara. Sarkin musulmi Muhammadu yana ganin Zamfarawa sun samu asali ne daga uba Bakatsine da uwa Bagobira. To su Zamfarawa sun kafa asalinsu daga Maguzawa maharba wadanda sun zauna a yankin kasar Kano kafin zuwan Bagauda tun kafin zuwan Barbushe a Dutsen Dala. A nan zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa Hausawa ne na asali tun can fil azal. Zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa dai asalinsu maharba ne daga Maguzawa. Watakila sun samu tasirin Bare- Bari a farkon tarihinsu ko kuma a ce Bare-bari na asalin sarautar Zamfara. Tarihin ƙauyen Zamfara ya samo asali ne daga mutum Na farko da ya fara zama a garin, daga garin ZAMFARA wanda ake kira da BAWA. Shi ya sa ake kiran garin da suna Zamfara. Farkon fadar masarautan an rusa ta. Garin ya haɗa iyakoki kamar haka; Rogo sabon gari da Tsohuwar Rogo ta gabas, Bari da Kaduna daga gefen yamma, Kaduna daga Kudu da Gari da Tsohuwar Rogo ta arewa.[1]
Ana ganin Zamfarawan asali wasu irin manya-manyan mutane ne, a takaice dai Samudawa ne. Dakka, sarkin Zamfara na farko kamar dai Barbushe yake, mutun ne mai tsananin girma da karfi da jarumta. Akwai wasu manya-manyan kaburbura guda shida a Dutsi wadanda aka ce kaburburan sarakunan Zamfara ne na asali. Sabo da girman kaburburan su ana kiransu da kaburburan Samudawa. Ga alamu Zamfarawa asali na da girman jiki sosai.
Birnin Zamfara
Zamfarawa sun fara kafa garinsu na farko ne mai suna Dutsi a kasar Zurmi ta yanzu. Don haka har yau Sarkin Zurmi na amsa sunan Sarkin Zamfara. An ce Zamfarawa sai da suka kwashe shekara bakwai ba su nada sarki ba a Dutsi,daga nan sai suka nada sarkinsu na farko mai suna Dakka.Don haka Sarkin Zamfara ana masa take da gimshikin gidan Dakka. Sarakuna hudu ne suka gaji Dakka a Dutsi. Daga nan sai sarauniyar 'Yar Goje.
Daga Dutsi sai Zamfarawa suka yi tafiyar kamar mil talatin a kan gulbin Gagare kusa da garin Isa na yanzu suka kafa wani sabon gari mai suna Birnin Zamfara. An ce Sarkin Zamfara na bakwai mai suna Bakurukuru ya kafa birnin. Amma wasu masana tarihi sun hakikance cewa sarakuna ashirin da uku 23 ne aka binne a garin Dutsi don haka ba dai sarki na bakwai ba wanda ya kafa Birnin Zamfara. Zamfarawa sun gina garinsu wanda ya habaka sosai. Sun katange shi da ganuwa.Har yanzu akwai kufan tsohon garin akwai rusasshiyar ganuwa mai tsawon milyan goma-sha-uku da kofofin gari hamsin. A nan zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa sun kafa garinsu na biyu wanda ya kasance babbar cibiyar mulkin Zamfara. Sannan garin ta samu arziƙin masarrafofin zamani irin su Makarantun Boko, islamiyya, rijiyoyi da kuma Burtsatse da dai sauransu.[1]Ofishin siyasa ta mata an buɗeta ne a garin zamfara a shekarar 2007. [2]
Kananan hukumomi[gyara sashe | Gyara masomin]
Rufe Netwok A Jihar Zamfara[gyara sashe | Gyara masomin]
A ranar 3 ga watan satumba na shekarar 2021, gwamnatin Jihar zamfara ta bada umarnin kulle dukkan layukan wayar hannu (sim cart) da sabis na daukacin Jihar zamfara gaba daya don a samu a magance matsalar tsaro. An yi hakan ne domin yaqi da 'Yan bindiga Dadi da kuma 'Yan ta'adda. An bada umarnin rufe sabis din ne na tsawon sati Biyu domin dawo da zaman lafiya da tsaro me dorewa a jihar.[3].
Bibilyo[gyara sashe | Gyara masomin]
- Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4.
- Bello, Ahmadu, Sir, 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu, Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman. Ismaila., Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle. ISBN 978-34637-2-1. OCLC 44137937.
- G.karaye, Ibrahim. J. Shea, Philip. History.of karaye. ISBN 978125341
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |
Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]
- ↑ 1.0 1.1 G.karaye, Ibrahim. J. Shea, Philip. History of karaye. p.71 ISBN 978125341
- ↑ Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. p.164 ISBN 978-978-906-469-4.
- ↑ https://punchng.com/banditry-months-after-no-fly-order-fg-shuts-down-telecom-sites-in-zamfara/