Jump to content

Joe Flaherty

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Joe Flaherty
Rayuwa
Haihuwa Pittsburgh (en) Fassara, 21 ga Yuni, 1941
ƙasa Tarayyar Amurka
Kanada
Mutuwa Toronto, 1 ga Afirilu, 2024
Karatu
Makaranta Central Catholic High School (en) Fassara
Point Park University (en) Fassara
Pittsburgh Playhouse (mul) Fassara
Westinghouse High School (en) Fassara
Humber College (en) Fassara
Sana'a
Sana'a dan wasan kwaykwayo mai magana amma ba a ganin shi a fim, dan wasan kwaikwayon talabijin, marubin wasannin kwaykwayo da humorist (en) Fassara
Kyaututtuka
Sunan mahaifi Joe Flaherty
IMDb nm0280886

Joseph "Joe" O'Flaherty (1941) dan wasan kwaikwayo ne, marubuci, kuma dan wasan barkwanci dan kasar Tarayyar Amurka. Ya yi fice da aikinsa na barkwanci na kasar Kanada mai suna sketch comedy SCTV daga 1976 zuwa 1984, wanda kuma ya kasance marubuci a wannan lokacin inda ya samu lambar yabo ta Primetime Emmy Award, rawar da ya taka a matsayin Harold Weir a cikin shirin Freaks and Geeks (1999), sannan kuma a matsayin heckler a cikin shirin Happy Gilmore (1996).

Kuruciya da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Joseph a June 21, 1941, a Pittsburgh, Pennsylvania, a matsayin dan fari cikin 'ya'ya bakwai.[1][2] Mahaifinsa ma'aikaci ne a wani kamfanin kere-kere mai suna Westinghouse Electric wanda yya fito ne daga kabilar Irish, sannan mahaifiyarsa ta fito ne daga kasar Italiya.

Joseph yayi aiki da Rundunar Sojoji Sama na Kasar Amurka na tsawon shekaru hudu, kafin ya fara aiki da gidan wasan kwaikwayo.[1]

Joseph ya koma Chicago inda ya fara wasan barkwancinsa a 1969 tare da gidan wasan kwaikwayo mai suna Second City Theater a matsayin Joe O'Flaherty, kuma yayi aiki tare da manyan 'yan wasa irinsu John Belushi da kuma Harold Ramis. Ya ajiye 'O' na cikin sunanshi saboda akwai wani jarumi mai irin sunan shi Joseph O'Flaherty.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


  1. 1.0 1.1 Hampson, Sarah (July 24, 2004). "The worrier in the comic mask". The Globe and Mail. Retrieved April 4, 2024.
  2. Holpuch, Amanda (April 2, 2024). "Joe Flaherty, 'SCTV' and 'Freaks and Geeks' Actor, Dies at 82". The New York Times. Retrieved April 4, 2024.