Jump to content

John Gomomo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
John Gomomo
Rayuwa
Haihuwa 1954
Mutuwa 2008
Sana'a
Sana'a trade unionist (en) Fassara

Phumzile John Gomomo (an haife shi a ranar 25 ga watan Oktoba na shekara ta 1945 - ya mutu a ranar 22 ga watan janairu na shekarar 2008) ɗan ƙungiyar tarayyar Afirka ta Kudu ne kuma ɗan gwagwarmaya.[1]

Fage da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Phumzile John Gomomo a gona a Adelaide a ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 1945, ɗaya daga cikin yara bakwai da marigayi Ndabeni (Mnzotho) da Nonga Stofile (Mpondo) suka haifa. Ya yi karatun firamare a Ntlaka Lower Primary School da Marry Mount High School. Ya bar makaranta a mataki na 6 (aji 8) saboda rashin yali, kuma daga baya ya kammala karatunsa ta hanyar kwasa-kwasan wasiƙa. Gomomo ya gudanar da ayyukan masana'antu da yawa a Uitenhage. A shekarar 1977, ya shiga ƙungiyar ma’aikatan motoci ta United, wadda daga baya ta haɗe da wasu ƙungiyoyin suka zama ƙungiyar ma’aikatan motoci da haɗin gwiwa ta ƙasa (NAAWU).

Yana aiki a Volkswagen a matsayin mai walda lokacin da ya zama shugaban kwamitin kula da shagunan masana'antar, inda ya jagoranci yajin aikin da aka yi a shekarar 1980 da 1982. An zaɓe shi shugaban shiyya na kungiyar ƙwadago ta Afirka ta Kudu me suna (FOSATU), wadda NAAWU ke da alaƙa da ita. A cikin shekarar 1986 ya kasance cikin tawagar Congress of African Trade Unions (COSATU) tawagar da suka gana da African National Congress (ANC) a Lusaka, kuma a shekarar 1989 ya sake kasancewa a cikin wata ƙungiya me suna COSATU da ta yi wa Nelson Mandela bayani a kurkuku.

Ya kasance memba na kwamitin kafa COSATU a shekarar 1985, [2] [3] kuma ya kasance shugaban wannan kungiyar daga shekarar 1991 zuwa shekarar 1999.[4]

Gomomo ya mutu a cikin shekara ta 2008 a Adelaide kuma an binne shi a can. Jana'izar sa ya samu halartar shugaban jam'iyyar ANC na lokacin Jacob Zuma da kuma shugaban Afirka ta Kudu na lokacin Thabo Mbeki da sauran manyan baki.

  1. Southall, Roger (2014). Opposition and Democracy in South Africa. Routledge. p. 194. ISBN 9781135277345.
  2. South African History Online. "Congress of South African Trade Unions (Cosatu)". South African History Online. Retrieved 15 July 2013.
  3. Cosatu. "Brief History of Cosatu". COSATU. Archived from the original on 27 June 2018. Retrieved 15 July 2013.
  4. Southall, Roger (2014). Opposition and Democracy in South Africa. Routledge. p. 194. ISBN 9781135277345.