Jump to content

John Mark Inienger

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Major General
John Mark Inienger
Haihuwa16 April 1945
Mbaduku, Vandeikya LGA, Benue State, Nigeria
Mutuwa8 Fabrairu 2002(2002-02-08) (shekaru 56)

John Mark Inienger (16 ga Afrilu, 1945 – 8 ga Fabrairu, 2002) Manjo Janar ne na Rundunar Sojin Najeriya wanda ya yi aiki a matsayin kwamandan rundunar ECOMOG a Laberiya, gwamnan mulkin soja na Bendel State tsakanin shekarun 1985 zuwa 1988, a lokacin gwamnatin soja ta Janar Ibrahim Babangida, sannan kuma ya kasance kwamandan Brigade of Guards.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Inienger a ranar 16 ga Afrilu, 1945 a Mbaduku, ƙaramar hukumar Vandeikya ta Benue State.[1]

Mahaifinsa ɗan Tiv ne daga Mbaduku, yayin da mahaifiyarsa ta fito daga Bebuabung a garin Obudu na Cross River State.[2]

Ya yi karatunsa na firamare a Makarantar Firamare ta Mkar tsakanin shekarun 1952 zuwa 1959. Daga nan ya halarci Nigerian Military School, Zaria daga 1960 zuwa 1963; makarantar Injiniyan Lantarki da Injiniyan Na'urorin Soja ta Najeriya da ke Lagos daga 1963 zuwa 1964; Nigerian Defence Academy da ke Kaduna a shekarar 1967; sannan ya yi karatu a Canadian Land Force Command and Staff College da ke Kingston, Ontario, Canada a shekarar 1974.[1][3]

Bayan kammala horonsa na gaggawa a Nigerian Defence Academy, Inienger ya yi yaƙi a Yaƙin Basasar Najeriya a Bataliya ta 22 ta Rundunar Ƙasa tsakanin shekarun 1967 zuwa 1969.[3] A wannan lokaci, kwamandansa shi ne Mamman Vatsa, sannan ya kuma ƙulla kusanci da Ibrahim Babangida, wanda ke aiki a wata runduna da ke makwabtaka da tasu.[4] Daga bisani ya zama kwamandan Bataliya ta 29 ta Rundunar Ƙasa a shekarar 1969.[3]

Bayan yaƙin, Inienger ya kasance kwamandan Bataliya ta 82 ta Rundunar Ƙasa daga 1970 zuwa 1973, malami a Makarantar Horar da Sojojin Ƙasa ta Najeriya daga 1975 zuwa 1976, sannan kwamandan Bataliya ta 31 ta Rundunar Ƙasa daga 1976 zuwa 1977. Ya kuma jagoranci Bataliyar Najeriya da aka tura ƙasar Lebanon tsakanin shekarun 1980 zuwa 1981, sannan ya zama kwamandan Rundunar 4 Mechanized Brigade daga 1984 zuwa 1985.[1]

A watan Agustan shekarar 1985, Janar Ibrahim Babangida ya zama shugaban mulkin soja na Najeriya bayan juyin mulki da ya hambarar da Muhammadu Buhari. Laftanar Kanal Inienger ya taka muhimmiyar rawa wajen wannan juyin mulki, kuma a matsayin lada aka naɗa shi gwamnan mulkin soja na Jihar Bendel, mukamin da ya riƙe har zuwa watan Disamban shekarar 1988.[5]

Daga baya ya yi aiki a matsayin kwamandan Brigade of Guards a Hedikwatar Rundunar Sojin Najeriya da ke Lagos (1988–1989), sannan ya zama kwamandan rundunar ECOMOG a Liberia daga 1993 zuwa 1996.[1]

A lokacin da yake jagorantar ECOMOG a Yaƙin Basasar Farko na Laberiya, al'amura sun kasance cikin ruɗani yayin da shugabannin ƙungiyoyin mayaƙa ke ƙoƙarin kwace yankuna domin samun fa'ida bayan an cimma yarjejeniyar zaman lafiya. An ruwaito Inienger yana cewa: "An shirya wani yaƙin ɓata suna domin a lalata martabar ECOMOG, tare da nuna cewa ba ta da tsaka-tsaki ko adalci... ana bayyana ECOMOG a matsayin rundunar mamaya."[6]

Zuwa watan Afrilun shekarar 1996, rundunarsa ta fuskanci matsananciyar ƙalubale wajen ci gaba da riƙe iko a babban birnin ƙasar, Monrovia, saboda mayaƙan sa-kai da ke gudanar da sace-sace da wawashe dukiyoyi.[7]

Inienger ya dawo daga Laberiya a shekarar 1996, sannan aka naɗa shi kwamandan Armed Forces Command and Staff College, Jaji.[1]

A watan Mayun shekarar 1999, gwamnatin soja ta miƙa mulki ga gwamnatin farar hula ƙarƙashin jagorancin Olusegun Obasanjo. Cikin wata guda bayan haka, sabuwar gwamnati ta umarci dukkan jami'an soja da suka yi aiki a gwamnatin soja fiye da watanni shida su yi ritaya.

Inienger na daga cikin jami'ai 100 da wannan mataki ya shafa.[8]

Ya rasu a ranar 8 ga Fabrairu, 2002 yayin da yake tafiya ta mota daga Jos zuwa Makurdi.[9]

  1. 1 2 3 4 5 Chidi 'Uzor in Lagos and Daniel Ior in Markurdi (2002-02-10). "Inienger, General, Former Governor Passes on". ThisDay. Archived from the original on September 10, 2005. Retrieved 2009-12-27.
  2. ↑ MAURICE ARCHIBONG (September 20, 2007). "In Vandeikya, inter-ethnic marriages fosters peaceful co-existence". The Sun. Lagos, Nigeria. Archived from the original on July 23, 2008. Retrieved 2009-12-27.
  3. 1 2 3 "INIENGER, Maj- Gen John Mark". Biographical Legacy & Research Foundation (BLERF). Retrieved 13 June 2026.
  4. ↑ Agbese, Dan (2012). Ibrahim Babangida: The Military, Politics and Power in Nigeria. Abuja, Nigeria: Adonis & Abbey Publishers. p. 97-8.
  5. ↑ MAX SIOLLUN (August 4, 2008). "The Babangida Years - Part 4". Nigeria Exchange News. Archived from the original on 2010-01-13. Retrieved 2009-12-27.
  6. ↑ Adekeye Adebajo (2002). Liberia's Civil War: Nigeria, Ecomog, and Regional Security in West Africa. Lynne Rienner. p. 131. ISBN 1-58826-052-6.
  7. ↑ JACKSON KANNEH (12 April 1996). "Looting orgy grips Monrovia". The Independent on Sunday. Archived from the original on 2022-06-13. Retrieved 2009-12-27.
  8. ↑ "Can a Military Coup Ever Succeed Again in Nigeria?". Max Siollun. April 11, 2008. Retrieved 2009-12-27.
  9. ↑ Daniel Ior (2002-02-24). "FG Immortalizes Inienger - Names cantonment after him". ThisDay. Archived from the original on April 19, 2005. Retrieved 2009-12-27.