Joseph Kignoumbi Kia Mboungou
2002 - | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Pointe-Noire, 10 Oktoba 1952 (73 shekaru) | ||
| ƙasa | Jamhuriyar Kwango | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa |
Pan-African Union for Social Democracy (en) | ||
Joseph Kignomba Kia Mbougou ɗan siyasan Kongo ne. Ya tsaya a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2002 na Pan-African Union for Social Democracy. [1] Ya zo na biyu mai nisa a zaben, inda ya samu kuri'u 33,154. [2]
Kignoumbi Kia Mbungou ya gaji Claudine Munari a matsayin sakatare na biyu na majalisar dokoki a ranar 22 ga watan Disamba 2009.
A zaɓen majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar a watan Yulin 2017 ya sake tsayawa takarar majalisar dokokin ƙasar a matsayin ɗan takarar La Chaine a mazaɓar ƙaramar hukumar Sibiti. Shi ne ya zo na ɗaya, da kashi 44% na kuri’un da aka kaɗa, a zagayen farko na zaɓen, sai ɗan takara mai zaman kansa, Jean-Favien Mabiala, wanda ya samu kashi 33.5%. [3] Ya lashe kujerar ne a zagaye na biyu na zaɓen. [4] A ranar 19 ga watan Agustan 2017, lokacin da majalisar dokokin ƙasar ta fara taron sabon wa'adinta, an sake zaɓen shi a matsayin sakataren majalisar na biyu. Shi ne ɗan takara ɗaya tilo, wanda shi ne kaɗai wurin da ofishin majalisar dokokin ƙasar ya keɓe domin ‘yan adawa, ya kuma samu kuri’u 142 daga wakilan da suka halarta. [5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "IFES Election Guide | Elections: Republic of Congo Presidential Mar 10 2002". www.electionguide.org. Retrieved 2021-08-31.
- ↑ "Elections in Congo-Brazzaville". africanelections.tripod.com. Retrieved 2021-08-31.
- ↑ "Les résultats tels que publiés par le ministre de l’intérieur et de la décentralisation", La Semaine Africaine, number 3,711, 25 July 2017, page 7 (in French).
- ↑ "Les resultats du second tour", Les Dépêches de Brazzaville, 4 August 2017, page 3 (in French).
- ↑ Bertrand Boukaka, "Congo – Assemblée Nationale : Isidore Mvouba accède au perchoir", Les Echos du Congo Brazzaville, 19 August 2017 (in French).