Joseph Utsev
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Jahar Benue, 1980 (45/46 shekaru) |
| ƙasa | Najeriya |
| Karatu | |
| Makaranta |
Jami'ar Najeriya, Nsukka University of Agriculture, Makurdi (en) |
| Harsuna | Turanci |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa |
Joseph Utsev ɗan siyasan Kasar Najeriya ne wanda ya fito ne daga Karamar Hukumar Buruku ta Jihar Benue dake Najeriya . Wanda a yanzu shi ne Ministan albarkatun ruwa da kuma tsabtace Najeriya.[1]
Rayuwarsa ta farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Utsev a ranar 2 ga watan Disambar shekarar 1980 a Jihar Benue, Najeriya . Ya kammala karatu daga Jami'ar Aikin Gona ta Tarayya, dake Makurdi inda ya sami digiri na farko a fannin Injiniyanci, ya kammala karatu tare da girmamawa na biyu wato "Upper Division" a shekarar 2004. [2] Ya kuma sami digiri na biyu ,da kuma digiri na uku wato PhD a fannin albarkatun ruwa da injiniyan muhalli daga Jami'ar Najeriya, Nsukka a cikin shekarun 2007 zuwa 2011.[3][4]
Rayuwarsa na aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Shugaba Bola Tinubu ne ya nada Utsev a matsayin ministan albarkatun ruwa da tsabta, a jamhuriyar Tarayyar Najeriya. Joseph Utsev yakasance malami ne kuma farfesa.[5]
A cikin shekarar 2017, ya kuma yi aiki a matsayin kwamishinan Ma'aikatar Ruwa da kulla da Muhalli na Jihar Benue . [6]
A cikin shekarar 2024, Ƙungiyar Kare Ruwa ta Afirka wato (AWCP) ta amince da Utsev saboda jagorancinsa wajen sarrafa albarkatun ruwa, tabbatar da rarraba daidaito, da inganta ayyukan masu ɗorewa.[7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Okogba, Emmanuel (2024-06-20). "Utsev: Harnessing Nigeria's Water Resources For Economic Gains". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2025-04-01.
- ↑ Okogba, Emmanuel (2024-06-20). "Utsev: Harnessing Nigeria's Water Resources For Economic Gains". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2025-04-01.
- ↑ Orokpo, Treasure (2023-07-27). "Who is Joseph Utsev: Biography of Utsev, age, family, education, career". Idoma Voice Newspaper (in Turanci). Retrieved 2025-04-01.
- ↑ press_admin (2024-02-15). "Education Profile of Joseph Ustev". PressPayNg Blog (in Turanci). Retrieved 2025-04-01.
- ↑ Orokpo, Treasure (2023-07-27). "Who is Joseph Utsev: Biography of Utsev, age, family, education, career". Idoma Voice Newspaper (in Turanci). Retrieved 2025-04-01.
- ↑ Okogba, Emmanuel (2024-06-20). "Utsev: Harnessing Nigeria's Water Resources For Economic Gains". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2025-04-01.
- ↑ Reporter, Our (2024-10-24). "Minister of Water Resource Joseph Utsev bags award". The Nation Newspaper (in Turanci). Retrieved 2025-04-01.