Jump to content

Josyline Kamateneti

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Josyline Kamateneti
Member of Parliament of Uganda (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Uganda, 16 ga Afirilu, 1982 (43 shekaru)
ƙasa Uganda
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa National Resistance Movement (en) Fassara
Kamateneti Josyline

Josyline Kamateneti 'yar siyasar ƙasar Uganda ce kuma 'yar majalisa. Ita 'yar majalisa ce mace a ƙarƙashin jam'iyyar National Resistance Movement for Ntungamo gundumar. [1] [2] Ita ma mamba ce a kwamitin ilimi da wasanni. [3]

Tarihin da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Josyline a ranar 16 ga watan Afrilu 1982 a ƙauyen Nyabushenyi, ƙaramar hukumar Nyabushenyi, gundumar Ntungamo zuwa marigayi Tadeo Kanyankore- Kakiga da Norah Twinomegisha. [4]

Josyline ta yi karatun firamare a Nyakisa Primary School, Horny High School - Kabale da Immaculate Heart Nyakibare girls secondary da matakin O' da A' bi da bi. [4] Ta kammala karatu daga jami'ar Makerere da digirin farko a fannin kasuwanci da ta kware a fannin kuɗi. [4]

Josyline ta yi aiki da bankin Crane kuma ta koma bankin Uganda inda ta yi aiki a matsayin akawu. [4]

Josyline ta auri Sande Baata-Kaketto kuma tana da ‘ya’ya 4. [4]

Bayanan siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Josyline Kamateneti ta tsaya takarar kujera a matsayin mace ‘yar majalisar wakilai a gundumar Ntungamo kuma ta zo ta ɗaya da kuri’u 156022, Natherine Matsiko Namara ta zo ta biyu da kuri’u 9175, Deborah Namara ta zo ta uku da kuri’u 4789 sai Sayuni Crinimh ya zo na huɗu da kuri’u 4641. [5]

  1. "Use AFCON to improve infrastructure, MPs tell Govt". New Vision (in Turanci). Retrieved 2024-04-30.
  2. ""Josyline Kamateneti" daily monitor - Google Search". www.google.com. Retrieved 2024-04-30.
  3. Isabirye, David (2021-09-22). "MP's tour Lugogo sports facility, hold brain storming meeting with National Council of Sports". Kawowo Sports (in Turanci). Retrieved 2024-04-30.
  4. 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 "Know your MP-elect: Joselyn Kamateneti". New Vision (in Turanci). Retrieved 2024-05-03.
  5. "WESTERN UGANDA'S FAILED MPS & HOW THEY PERFORMED INSIDE THE 2021 BALLOT BOX". mulengeranews.com (in Turanci). 2023-09-11. Retrieved 2024-04-30.[permanent dead link]