Jump to content

Judith Alyek

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Judith Alyek
Member of the Parliament of Uganda (en) Fassara

2016 -
Joy Ruth Acheng (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Uganda, 8 Oktoba 1971 (53 shekaru)
ƙasa Uganda
Karatu
Makaranta Atan Primary School (en) Fassara
Jami'ar shahidan Uganda
Jami'ar Musulunci a Uganda
Cibiyar Gudanarwa ta Uganda
Jami'ar Makerere
Jami'ar Clarke ta Duniya
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a health professional (en) Fassara, ɗan siyasa da HIV/AIDS activist (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa National Resistance Movement (en) Fassara

Judith Alyek (an Haife ta a ranar 8 ga watan Oktoba 1971) 'yar siyasar ƙasar Uganda ce kuma Wakiliyar Mata ta gundumar Kole a Majalisar 10th ta Uganda. Ita mamba ce a jam'iyyar National Resistance Movement wacce ta samu tikitin tsayawa takara a zaɓen shekara ta 2016. Ta kuma kasance shugabar kwamitin yaki da cutar kanjamau da cututtuka masu alaka da su. [1] [2]

A majalisa ta goma sha ɗaya tana aiki a kwamitin daidaita damammaki. [3]

Tarihi da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Judith Alyek ta halarci firamare a makarantar firamare ta Atan a gundumar Kole. A tsakanin shekarun 1987 zuwa 1990, ta halarci St. Catherine SS a Lira don shaidar takardar ta matakin O kuma ta sami UACE daga Kwalejin Dr. Obote, Boroboro a shekarar 1993.

Ga cikakken tarihin aiki na Alyek: [4]

  • 2016 zuwa yau : Wakilin Mata na gundumar Kole
  • 2011-2015 : Mashawarciyar Fasaha, Lafiyar Mata da Yara, HIV/AIDS da Abinci, Gidauniyar AVSI
  • 2007-2010 : Babbar Malamar Lafiya, a Ƙaramar Hukumar Dokolo
  • 2000-2006 : Sufeto Lafiya, a ƙaramar hukumar Lira

Ta yi aiki a kan ƙarin aikin Majalisar Uganda: [4]

  • Shugaban - Kwamitin kan HIV/AIDS da cututtuka masu alaƙa [4]
  • Memba - Kwamitin Kasuwanci
  • Memba - Kwamitin Lafiya
  • Memba – Ƙungiyar Majalisun Mata ta Uganda (UWOPA) [5] [1]
  • Memba - Hukumar Kula da Agaji ta Uganda [6]
  • Majiɓinci - SERVE Uganda [7] [2] Archived 2023-03-19 at the Wayback Machine Archived
  • Memba - Ƙungiyar Ci gaban Lafiya da Ilimi ta Duniya (IUHPE) Archived 2023-03-21 at the Wayback Machine

Gwagwarmaya

[gyara sashe | gyara masomin]

A matsayinta na shugabar kwamitin yaki da cutar kanjamau da cututtuka masu nasaba da cutar, ta yi kira da a yi wa maza gwajin cutar kanjamau dole. Ta kuma yi kira ga shugabannin yankin da su bayyana halinsu na HIV a matsayin misali ga mutanen da suke shugabanta. [8]

A watan Yulin 2017, ta gabatar da kudirin aiwatar da dukkan manufofi da dokoki da suka shafi yara. [9] Ta buƙaci kafa wata hukuma da za ta saukaka lura da aiwatar da hakkokin yara [10]

A sakamakon mutuwar Dickens Okello a cikin shekarar 2018, [11] ta buƙaci 'yan majalisa daga yankin Lango da su sake duba tare da ba da shawarar matakan da za a ɗauka a kan "Indiyawa da ake zargi da take hakkin mutanen Lango." [12]

A cikin shekarar 2017, Alyek ta yi ikirarin cewa ta auri Richard Odongo kuma ta musanta ikirarin da mataimakin sarkin ƙabilar Inomo ta yi cewa Ambrose Eger, wacce ta rasu a lokacin, mijinta ne. [13]

  • Gundumar Kole
  • Jerin sunayen 'yan majalisar dokoki na goma na Uganda
  • Majalisar Uganda

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. "Alyek Judith - 2021 General Election - Visible Polls". visiblepolls.org (in Turanci). Retrieved 2023-02-09.
  2. "Judith Alyek". theyworkforyou.github.io. Retrieved 2023-02-09.
  3. "Committee on Equal Opportunities – Parliament Watch" (in Turanci). Retrieved 2023-02-09.
  4. 4.0 4.1 4.2 "Parliament of Uganda". parliament.go.ug. Archived from the original on 21 March 2018. Retrieved 13 March 2019.
  5. "Members of UWOPA of 10th Parliament | Uganda Women Parliament Association". uwopa.or.ug. Archived from the original on 18 April 2021. Retrieved 13 March 2019.
  6. "The Board". aidsuganda.org. Retrieved 15 March 2019.
  7. "About Us -Sustainable Effort for Rural Vulnerable-group Empowerment". serve.ug. Archived from the original on 19 March 2023. Retrieved 13 March 2019.
  8. "Leaders on the spot on HIV disclosure". The Independent Uganda. 8 November 2018. Retrieved 13 March 2019.
  9. "MPs root for creation of Childrens' [sic] Authority". theinsider.ug. Archived from the original on 22 July 2017. Retrieved 15 March 2019.
  10. "MPs root for creation of Childrens' [sic] Authority". Uganda Mirror. 5 February 2018. Retrieved 15 March 2019.
  11. "Two arrested over murder of 11-year-old pupil". Daily Monitor. Retrieved 13 March 2019.
  12. "Two men held over death of pupil". newvision.co.ug. Retrieved 13 March 2019.
  13. "MP disowns dead husband". Daily Monitor. Retrieved 13 March 2019.