Justine Lumumba Kasule
Justine Lumumba Kasule malama ne kuma 'yar siyasa 'yar ƙasar Uganda. Ita ce Minista na yanzu, Ofishin Firayim Minista (General Duties), a cikin majalisar ministocin Uganda, tun watan Yuni 2021. [1]
Kafin haka, ta kasance Sakatare Janar na National Resistance Movement, jam'iyyar siyasa mai mulki a Uganda. An naɗa ta a wannan matsayi a ranar 23 ga watan Disamba 2014, ta maye gurbin Amama Mbabazi. [2] Kafin wannan lokacin, ta yi aiki a matsayin Babbar Jami'iyar Gwamnati a Majalisar Dokokin Uganda daga watan Mayu 2011 zuwa watan Disamba 2014. Justine Lumumba Kasule kuma ta kasance zaɓaɓɓiyar 'yar majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Bugiri daga shekarun 2001, har zuwa lokacin da ta yi murabus a watan Disamba 2014.[3]
Tarihi da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haife ta a gundumar Bugiri a ranar 22 ga watan Nuwamba 1972. Ta halarci Makarantar Sakandare ta St.[3] Anthony a Nkokonjeru don karatun matakin O. Daga nan ta koma makarantar sakandire ta St. Joseph da ke Naggalama, don karatunta na A-Level. A cikin shekarar 1993, an shigar da ita Jami'ar Makerere, inda ta kammala digiri na farko a fannin fasaha tare da difloma a lokaci guda a fannin ilimi, a shekarar 1996. [3] [4]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Daga shekarun 1996 zuwa 1997 ta yi aiki a matsayin malama. Daga shekarun 1997 zuwa 1998, ta yi aiki a matsayin Mukaddashiyar Sufeto a Makarantun gundumarta. Daga shekarun 1998 zuwa 2001, ta yi aiki a matsayin babbar jami'ar ilimi a ma'aikatar ilimi. A cikin shekarar 2001, an zaɓe ta zuwa majalisar dokoki, a kan tikitin jam'iyyar siyasa ta National Resistance Movement, don zama wakiliyar mata na gundumar Bugiri. An sake zaɓen ta daga shekarun 2001 zuwa 2014, lokacin da ta sauka daga muƙamin sakatariyar jam'iyyar siyasa ta National Resistance Movement mai mulki. [3] [5] A cikin watan Mayu 2011, an naɗa ta a matsayin Babbar Jami'iyar Gwamnati, wacce ta maye gurbin John Nasasira. [4] [6]
Sauran la'akari
[gyara sashe | gyara masomin]Ita uwa ce mai aure sannan tana da 'ya'ya maza biyu. Ita 'yar Roman Katolika ce.[4]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Majalisar ministocin Uganda
- Majalisar Uganda
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Uganda State House (8 June 2021). "Full Cabinet List 2021". Uganda Media Centre. Archived from the original on 12 February 2022. Retrieved 12 February 2022.
- ↑ Olive Nakatudde (23 December 2014). "Justine Lumumba Appointed NRM Secretary General". Uganda Radio Network. Retrieved 14 February 2015.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 Kakaire, Sulaiman (24 December 2014). "The new faces of NRM: Justine Kasule Lumumba - Secretary General". The Observer (Uganda). Kampala. Retrieved 30 October 2016.[permanent dead link]
- ↑ 4.0 4.1 4.2 Administrator (3 March 2013). "Justine Kasule Lumumba: The Yellow Girl From Bugiri". Archived from the original on 15 February 2015. Retrieved 30 October 2016.
- ↑ Red Pepper Staff (23 December 2014). "Justine Kasule Lumumba, the government Chief Whip has been appointed the Secretary General of the ruling National Resistance Movement party replacing former Prime Minister Amama Mbabazi". Retrieved 30 October 2016.
- ↑ New Vision (27 May 2011). "Comprehensive list of new Cabinet appointments + dropped ministers". Facebook. Retrieved 30 October 2016.