Jump to content

Kunun tsamiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga KUNUN TSAMIYA)
Kunun tsamiya
Kayan haɗi tsamiya, gero, sukari, peppercorn (en) Fassara da citta

Kunun tsamiya, yana Daya daga cikin abincin Bahaushe a kasar Hausa wanda mafi akasari aka fi amfani dashi ko in ce aka fi shan sa da zarar hantsi ya dubi ludayi lokacin walaha (hantsi) mafi lokuta yayin aikin gona, bikin aure, suna kai har ma da makwalla-makwalla. Kunun tsamiya dai abin sha ne mai kauri wanda ake yin sa da garin gero,da farko dai za,a sami gero sai a surfashi bayan an surfa sai a wanke shi sai a markadashi idan an markadashi sai a tace shi sai a sami kayan kanshi irin su barkono kanunfari citta masoro da tsamiya ko lemon tsami bayan an tace shisai a zuba wadannan kayan kamshin bayan an dakasu sai a zuba a ciki sai a dafa tafasasshen ruwa. Ana yi masa gaya ta hanyar kwaba garin ya yi dan tauri-tauri sai a jefa cikin tafasasshen ruwan nan. Bayan an kuma kwaba garin da jikakken ruwan tsamiya, ko lemon tsami sai a zuba shi a masaki (kwarya-babba) a dama shi ruwa-ruwa, kauri-kauri, sai a kawo wannan tafasasshen ruwan na kan wuta a zuba a cikin damammen garin nan mai ruwan tsamiya sai a juya da babban ludayi za a ga ya yi kauri kirtib. a na iya shansa da sukari ko a haka Shi Kuma ya sa Bahaushe yake yi masa take da cewa kunu na tsula tsafin mata.[1][2][3][4].

  1. https://www.yaurimedia.com.ng/2019/01/gero-gargajiyance-b.html[permanent dead link]
  2. https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
  3. https://cookpad.com/ng/recipes/6557695-kunun-tsamiyatamarind-pap
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-10-31. Retrieved 2020-12-27.