Kaigara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kai-gara dai wata al'ada ce da malam bahaushe kan gudanar da ita a lokacin da akayi aure.

Yaushe ake kai gara[gyara sashe | gyara masomin]

A rana ta huɗu ne da hantsi yan'uwan amarya da sauran abokin arziƙi kan kaigara tare da yin kafi na kanta da liki na farantai da tasoshi kuma ayi jeren ƙwanoni da kambuna. A wannan ranar da yamma ne akewa amarya wanka, akan fito da amarya tsakar gida a tuɓuta tsirara sannan a zaunar da ita akan turmi a sanya mata goro farare guda uku (3) akan sanya mata a bakinta ta gumtse sannan a rinƙa mata waƙa, ana waƙa ana mata wanka da ruwan rijiyoyi bakwai (7) na gidajen da ake zaton ba'a taɓa yaji ba. [1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-01-24. Retrieved 2021-03-12.