Kambodiya
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
កម្ពុជា (km) | |||||
|
|||||
![]() | |||||
| |||||
Take |
Nokor Reach (en) ![]() | ||||
| |||||
Kirari | «ជាតិ សាសនា ព្រះមហាក្សត្រ» | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Phnom Penh | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 16,005,373 (2017) | ||||
• Yawan mutane | 88.41 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati |
Khmer (en) ![]() | ||||
Addini | Buddha | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na |
Southeast Asia (en) ![]() | ||||
Yawan fili | 181,035 km² | ||||
Wuri mafi tsayi |
Phnom Aural (en) ![]() | ||||
Wuri mafi ƙasa |
Thailand (en) ![]() | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Ƙirƙira | 9 Nuwamba, 1953 | ||||
Muhimman sha'ani | |||||
Tsarin Siyasa | |||||
Tsarin gwamnati |
constitutional monarchy (en) ![]() | ||||
Gangar majalisa |
Parliament of Cambodia (en) ![]() | ||||
• King of Cambodia (en) ![]() |
Norodom Sihamoni (en) ![]() | ||||
• Prime Minister of Cambodia (en) ![]() |
Hun Sen (en) ![]() | ||||
Ikonomi | |||||
Kuɗi |
riel (en) ![]() | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Suna ta yanar gizo |
.kh (en) ![]() | ||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +855 | ||||
Lambar taimakon gaggawa |
119 (en) ![]() ![]() ![]() | ||||
Lambar ƙasa | KH | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | tourismcambodia.com |
Kambodiya ƙasa ce da ke kudu maso gabashin Asiya kuma ta na da jama'a da yawansu ya haura miliyan 13. Sunan babban birnin ƙasar Phnom Penh. Kambodiya ta samo asali ne daga daular Hindu da Buddha, wadda ta mulki yankunan Indonesiya da China tsakanin ƙarni na 11 zuwa ƙarni na 14.
Yawancin ‘yan ƙasar Kambodiya mabiya addinin Buddha ne, amma kuma akwai musulmi da dama da chinese ‘yan asalin ƙasar, da yan asalin ƙasar Vietnam da kuma yan tsirarun yarurruka da ke zaune akan tsaunuka.
Ƙasar Kambodiya na maƙwabtaka da ƙasashen Thailand a yammaci da kuma yamma maso arewa, Laos a arewa maso gabas da Vietnam a gabas da kudu maso gabas. A kudu tana fuskantar kogin Thailand.
Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]
Siyasa a ƙasar Kambodiya ta kafu ne akan tafarkin kundin tsarin mulkin ƙasar na 1993, kuma tsari ne da aka yi da ke da Sarki da kuma Firaminista, waɗanda wakilan jama'a ne ke zaɓansu. Firaministan ƙasar shi ne shugaban gwamnati, wadda ta ƙunshi jam'iyyu dabam-dabam, a yayin da kuma sarki shi ne shugaban ƙasa. Sarki ne ke naɗa Firaminista tare da shawara da kuma yardar majalisar ƙoli ta ƙasar. Firaminista tare da ministocin sa na da ikon zartar da doka a gwamnati, a yayin da alhakin tsara dokoki ya rataya ne akan majalisun dokoki da kuma ɓangaren masu zartar da dokar.
A ranar 14 ga watan Oktoba, wata majalisa ta musamman mai wakilai 9, ta zaɓi Sarki Norodom Sihamoni, a wani tsari na zaɓe da aka yi cikin gaggawa, sati ɗaya bayan Sarki Norodom Sihanouk (1922 – 2012), ya ƙi amincewa. Zaɓen sarki Sihamoni ya sami albarkacin Firaminista Hun Sen da shugaban majalisar dokokin ƙasar, Norodom Ranariddh, waɗanda dukkan su wakilai ne a majalisar zaɓen sarki. An rantsar da sabon sarkin ne a ranar 29 ga watan Oktoba, a babban birnin Kambodiya, wato Phnom Penh.
Masana'antun ƙasar Kambodiya dai sune na sutura, yawon shaƙatawa da kuma gine-gine. A shekara ta 2007, yawan baƙin da suka ziyarci ƙasar daga ƙasashen waje ya haura miliyan biyu. An gano mai da albarkatun ƙasa a ƙarkashin ruwan dake zagaye da ƙasar a shekara ta 2005, kuma idan aka fara zaƙulo waɗannan albarkatun ƙasa a shekara ta 2011, to ana ganin cewa kuɗin shigan da za a riƙa samu daga Man zai haɓaka arziƙin ƙasar ta Kambodiya
Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
Asiya | |||
Kazakystan • Kyrgystan • Tajikistan • Turkmenistan • Uzbekistan |
Sin • Japan • Mangolia • Koriya ta Arewa • Koriya ta Kudu • Jamhuriyar Sin | ||
Armeniya • Azerbaijan • Baharain • Georgia • Irak • Isra'ila • Jordan • Kuwait • Lebanon • Oman • Qatar • Saudiyya • Siriya • Turkiya • Taraiyar larabawa • Falasdinu • Yemen | Brunei • Kambodiya • Indonesiya • Laos • Maleshiya • Myanmar • Filipin • Singafora • Thailand • Timor-Leste • Vietnam | ||
Afghanistan • Bangladash • Bhutan • Indiya • Iran • Maldives • Nepal • Pakistan • Sri Lanka |