Jump to content

Kame Aden(1548)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentKame Aden(1548)

Map
 12°48′N 45°01′E / 12.8°N 45.02°E / 12.8; 45.02
Iri faɗa
Bangare na Ottoman–Portuguese conflicts of 1538–1560 (en) Fassara
Kwanan watan 26 ga Faburairu, 1548
Wuri Aden (en) Fassara
Ƙasa Yemen
Participant (en) Fassara

Kame Aden na 1548 ya cika ne a lokacin da daular ottoman karkashin Piri Reis suka yi nasarar kwace tashar jiragen ruwa na Aden a Yemen daga 'yan fotigal a ranar 26 ga Fabrairu 1548.[1]

Tuni daular Ottoman ta kama Aden domin Suleman mai girma a shekara ta 1538 ta hannun Hadim Suleiman Pasha, domin ya samar da sansanin daular Ottoman don kai farmaki a kan kadarorin 'yan fotigal a yammacin gabar tekun Indiya.[2] Da suke tafiya zuwa Indiya, daular Ottoman ta kasa cin nasara a kan Turawan Fotigal a sanda sojojin daular Ottoman suka zagaye Diu dan hana shigar kayayyaki a watan Satumba na shekara ta 1538, amma sai suka koma Aden inda suka karfafa birnin da manyan bindigogi 100.[3][4]

Daga wannan sansani Sulayman Pasha ya sami nasarar karbe iko da kasar Yemen baki daya, kuma ya karbe Sanaa. A cikin 1547, Aden ta tashi don yakar daular Ottoman amma ta gayyaci 'yan fotigal a maimakon haka, ta yadda 'yan fotigal ke iko da birnin.[5]

Ali bin Suleyman al-Tawlaki wanda wani basarake ne na yankin ya yi yaki da sojojin ruwan Daular Ottoman dake a jiragen ruwa 60 masu girma dabam-dabam wadanda suka iso a ranar 15 ga Nuwamban 1547 har zuwa rasuwarsa, sannan dansa Mohammed ya gaje shi, wanda ya ci gaba da yin turjiya har sai da wata karamar tawagar jiragen ruwa na kasar Portugal me dauke da Jiragen ruwa guda 3 suka iso a ranar 19 ga Janairun 1548. Duk da haka, an tilasta wa 'yan Fotigal komawa baya zuwa Zeila, inda aka kama masu ma’aikatan jirgin ruwa 120, kuma aka kona jiragensu. Daga karshe, Daular Ottoman sun yi nasara kuma Piri Reis ya kwace birnin a ranar 26 ga Fabrairun 1548.[6]

  1. Ezel Kural Shaw (29 October 1976). History of the Ottoman Empire and modern Turkey. pp. 106–107. ISBN 9780521291637.
  2. The history of Aden, 1839-72 by Zaka Hanna Kour p. 2
  3. The history of Aden, 1839-72 by Zaka Hanna Kour p. 2
  4. Halil İnalcik (May 1997). An economic and social history of the Ottoman Empire. p. 326. ISBN 9780521574563.
  5. R. B. Serjeant, The Portuguese off the South Arabian Coast, Hadrami Chronicles, Oxford, 1963, p. 20.
  6. Ertuğrul Önalp (12 December 2013). "Pîrî Reis'in Hürmüz Seferi ve İdamı Hakkındaki Türk ve Portekiz Tarihçilerinin Düşünceleri" [The Military Expedition of Piri Reis to Hormuz and the Considerations of Turkish and Portuguese Historians About his Execution] (PDF) (in Turkish). p. 5. Archived from the original (PDF) on 12 December 2013.