Jump to content

Karatu da rubutu a Somaliya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Karatu da rubutu a Somaliya
Bayanai
Ƙasa Somaliya
A black girl wearing a purple hijab pointing and reading Somali text off of a chalkboard
Wata yarinya tana karatu daga allon rubutu a Mogadishu

Somaliya kasa ce da ke yankin kahon Afirka mai yawan jama'a kusan miliyan goma sha tokwas 18. [1] As of 2022 Kasar tana da yawan masu karatun boko kusan kashi 41%. [2] [3] Akwai gagarumin bambanci tsakanin jinsi a yawan karatu, tare da 54% na maza kuma 22% na mata ne kawai suke da ilimi. [4] [5] A cewar USAID, yawan ilimin matasa ya kai kusan 70%. [6] Harsunan hukuma na Somaliya su ne Somaliya da Larabci, tare da Ingilishi da Italiyanci kuma. [6]

Abubuwan da ke tattare da karatu da rubutu

[gyara sashe | gyara masomin]

Ilimi a Somaliya ba ya yaduwa, tare da kusan kashi 85% na yara da ba su shiga makaranta ba bisa ga USAID.[7] Kasar tana da ƙarancin kammala karatun sakandare na 19.5%.[8] Rashin ilimi na Somaliya da ƙarancin ƙwarewa an danganta su da tasirin Yaƙin basasar Somaliya da ke gudana, wanda ya fara a kusa da shekara ta 1991.[9] Duk da wannan, yawan mutanen da ke karatu da rubutu na yanzu na 41% ci gaba ne daga 24% a cikin 1990, kuma kafin haka, 5% a cikin 1972. [10][9]

Yankunan da ke da ikon cin gashin kansu

[gyara sashe | gyara masomin]

Yankunan Puntland da Somaliland jihohi ne masu zaman kansu waɗanda suka rabu da Somaliya sakamakon yakin basasar Somaliya.[11][12] Ya zuwa 2013, Puntland tana da yawan karatu da rubutu na 72% kuma Somaliland tana da ɗaya daga cikin 44%. [lower-alpha 1] An danganta ilimin karatu da rubutu da zama a cikin birni, kuma bambancin da ke tsakanin yankuna an danganta shi da mafi yawan mutanen Puntland da suka kammala makarantar firamare ko halartar madrasa.

  1. In this report, "illiterate" was given as a level of education; literacy values are derived from the percentage of illiterate respondents.[13]
  1. "Somalia". UNICEF. Retrieved 3 August 2024.
  2. "Literacy Rate, Adult Total". World Bank Group. Retrieved 3 August 2024.
  3. "Country Profile: Somalia" (PDF). United Nations. Retrieved 3 August 2024.
  4. "Literacy Rate, Adult Male". World Bank Group. Retrieved 3 August 2024.
  5. "Literacy Rate, Adult Female". World Bank Group. Retrieved 3 August 2024.
  6. 6.0 6.1 "Somalia - Education - Literacy". USAID. Archived from the original on 3 August 2024. Retrieved 3 August 2024.
  7. "Somalia - Education and Health" (PDF). USAID. Archived from the original (PDF) on 3 August 2024. Retrieved 3 August 2024.
  8. "Country Profile: Somalia" (PDF). United Nations. Retrieved 3 August 2024.
  9. 9.0 9.1 Hassan, Mohamed (23 July 2020). "Literacy in Somalia: A Struggle to Rebuild the System Broken by War". DevelopmentAid (in Turanci). Retrieved 3 August 2024.
  10. "Literacy Rate, Adult Total". World Bank Group. Retrieved 3 August 2024.
  11. "Puntland Profile". BBC News. 3 April 2024. Retrieved 3 August 2024.
  12. "Somaliland Profile". BBC News. 2 January 2024. Retrieved 3 August 2024.
  13. "Family Ties: Remittances and Livelihoods Support in Puntland and Somaliland" (PDF). Food Security and Nutrition Analysis Unit - Somalia. 5 June 2013. p. 6. Retrieved 3 August 2024.