Kariman Hamza
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Kairo, 8 ga Faburairu, 1942 |
| ƙasa |
Kingdom of Egypt (en) Republic of Egypt United Arab Republic (en) Misra |
| Mutuwa | 31 Disamba 2023 |
| Karatu | |
| Makaranta | Jami'ar Alkahira |
| Harsuna | Larabci |
| Sana'a | |
| Sana'a |
publicist (en) |
Kariman Hamza (8 ga Fabrairu 1942 - 31 ga Disamba 2023) ƴar jaridar Masar ce kuma mai gabatar da shirye-shiryen shirin Talabijin. Ta yi aiki a fannin shirye-shiryen addini a talabijin daga 1970 zuwa 1999. Mahaifinta shine Abdul Latif Hamza, farfesa a fannin jarida a sashen Bayanai.[1] Ita ce mai watsa shirye-shirye ta farko a gidan talabijin na Masar.[2]
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Hamza ta fara aiki ta hanyar gabatar da shirin yara mai taken "Alkur'ani na Ubangijinmu". Ta gabatar da shirye-shiryen talabijin sama da 1,500 a tsawon shekarun aikinta tare da malaman addinin Islama daban-daban da ta gabatar da shirye-shiryen da su,aciki har da Sheikh Yusuf Al-Qaradawi, Sheikh Muhammad Al-Ghazali, da Sheikh Muhammad Metwally Al-Shaarawi, ban da rubuta littattafai da yawa da ta yi, ciki har na: من الله, زامري, نيجار And الغابة Cid الخلق. Har ila yau, ta gabatar da wasu shirye-shiryen da yawa kamar su: الرضا والنور, بالحق أنزلنا, وبالحق نزل, .
Hamza ta rubuta kundin "الأناقة والتواضع," wanda ke nuna wasu tufafi masu kyau na mata masu rufe fuska.[3] Ta yi aiki a tashar talabijin ta Iqra kuma ta yi aikin fassarar Alkur'ani ga matasa a ƙarƙashin taken "تفسير القرآن الواضح للشباب".
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "تشييع جثمان الإعلامية كاريمان حمزة إلى مثواها الأخير - اليوم السابع". 1 January 2024. Archived from the original on 1 January 2024. Retrieved 26 January 2024.
- ↑ "وفاة كاريمان حمزة أول مذيعة محجبة في التلفزيون المصري | منوعات | الجزيرة نت". 3 January 2024. Archived from the original on 3 January 2024. Retrieved 26 January 2024.
- ↑ "كيف ظهر «البوركينى» فى مصر؟ - الوطن". 6 April 2023. Archived from the original on 6 April 2023. Retrieved 26 January 2024.