Jump to content

Karramawa na Elizabeth II

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Karramawa na Elizabeth II
coronation of the British monarch (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Birtaniya
Muhimmin darasi Elizabeth II
Kwanan wata 2 ga Yuni, 1953
Participant (en) Fassara Elizabeth II
Wuri
Map
 51°29′58″N 0°07′39″W / 51.4994°N 0.127367°W / 51.4994; -0.127367

karramawa da Nadin Gimbiya Elizabeth ta biyu a matsayin sarauniya na Ƙasar Ingila da sauran yankunan kasashen Commonwealth ya faru ne a ranar 2 ga Yuni 1953 a Westminster Abbey a garin Landan. Gimbiya Elizabeth ta hau gadon sarauta tana da shekaru 25 a duniya bayan mutuwar mahaifinta, George VI, a ranar 6 ga Fabrairu 1952, inda aka ayyana ta a matsayin sarauniya ta majalisun sirri da zartarwa jim kadan bayan mutuwar mahaifin ta. An gudanar da karramawamar ta fiye da shekara guda bayan haka saboda al'adar ba da damar tsawon lokacin da ya dace ya wuce bayan sarki ya mutu. Har ila yau, kwamitocin tsare tsare mulki sun samu tsara isasshen lokaci don yin shirye-shirye don bikin.[1] A lokacin hidimar, Sarauniya Elizabeth ta yi rantsuwa ta gudanar da aiki an shafamata ta Mai, Mai Tsarki, an saka ta da riguna da haba ado, kuma an naɗa ta Sarauniya ta Ingila, Kanada, Ostiraliya. [2]

An gudanar da bukukuwan nadinta duk faɗin kasashen Commonwealth kuma tasamu lambar yabo ta tunawa. Ita ce ta farko da aka naɗa ta Burtaniya wadda aka nuna a gidan talabijin; ba a yarda da kyamarorin talabijin a cikin masallacin ba a lokacin da iyayenta suka naɗa ta a 1937. Elizabeth ita ce ta huɗu kuma ta ƙarshe ta mallaki Burtaniya a karni na 20. An kiyasta cewa an kashe kudi zunzurutu dasuka Kai kimanin uro dala 1.57 miliyan a kiyasi na kudin kasar ingila

  1. "60 Fascinating Facts About The Queen's Coronation". Royal Central. 1 June 2013. Archived from the original on 17 July 2020.
  2. "The coronation and visit of Queen Elizabeth II". Museum of New Zealand. New Zealand Government. Retrieved 4 May 2024.