Kiɗan ƙwarya
Kiɗan ƙwarya ko Kiɗan Amada wannan wani nau'in kiɗa ne da ake yin shi a arewacin Najeriya nishaɗi, ne a kan gudanar da shi ta amfani da ƙwaraye da kananan sanduna, ƙoren ana kifa su ne ko dai a ƙasa ko cikin robar ruwa, sannan ana bugun su da hannu ko sandunan da ake kira makaɗi, ana hakan sai ka ji tana bada sauti mai daɗi, tsofaffin mata suke yin Kiɗan.
Yawancin Waƙoƙin Kiɗan ƙwarya ko amada suna fadakar da mata ne wani lokacin ma har da mazaje, a kan neman ilimi, da yin sana'o'in hannu da kuma nunin illar zaman kashe wando, ta hanyar raha da yin tsokana akan kishiyoyi da ke gidajen aure. Wannan hanya ce ta nishadi daga cikin al'adun Hausawa, kuma an fi gudanar da shi ne a lokacin biki, walau aure ko bidiri, haka kuma a kan gudanar da Kiɗan ƙwarya lokacin bikin suna.