Kisan Gillar Hausawa a Jihar Edo
Appearance
Kisan gillar Hausawa a jihar Edo yana nufin wani mummunan kisan kiyashi ne da aka yiwa wasu mafarauta ƴan Areawa ya faru a ranar 28 ga watan Maris shekara ta 2025 a Udune Efandion al'ummar Uromi, karamar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas, jihar Edo, Najeriya. Wasu gungun ƴan ta'adda sun kashe mutane guda 16, kuma dukkanninsu Hausawa ne mafarauta daga arewacin Najeriya, batare da wani laifi ba, wanda kawai suna zargin ko masu garkuwa da mutane ne. Ƴan bijilantin yankin ne suka tare matafiyan da lamarin ya rutsa da su, inda suka ga kayan farautarsu irin na gargajiya irin su bindiga harba-ruga, barandami, wuƙaƙe da dai sauransu. Lamarin da ya kai ga yasa nan take a fara Dukansu har aka tara su waje ɗaya aka ƙona su.[1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Yusuf, Bada (2025-03-28). "Edo Massacre: How 16 Northerners Were Killed Over False Allegations - Legit.ng". www.legit.ng (in Turanci). Retrieved 2025-03-29.