Kiwo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Kiwo shine aikin da ya kunshi rainon dabbobi domin cin gajiyarsu ko amfana daga garesu, ta hanyar amfani da abinda suke samarwa kamar nama, gashi, mai, nono, Kashi, kwai dadai sauransu. Kiwo ya hada da kula da dabbobi ko neman karin yawansu dan saidawa da basu abinci, da basu magani. A duk fadin duniya al'ummomi daban-daban nada ire-iren hanyoyin da suke kiwota dabbobinsu kuma yabanbanta da na wasu al'umman, hakazalika mafiya yawan dabbobin da aka fi kiwota su a duniya sune dabbobi kamar; Saniya, Tumaki, Akuya, Kaji, Aladu, Kifaye da sauransu. Harwayau akwai wasu nau'ukan dabbobi da ake kiwitasu a wasu bangaren duniya, kamar Doki, Zomo, Zuma, kunkuru, Tsintsaye da sauransu. Wadanda ayanzu suke yaduwa a duniya kuma kusan kowa na kiwotasu.