Jump to content

Ƙofar Ƙwaya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Kofar Kwaya)
Kofar Kwaya
Ƙofar Kwaya

Kofa kwaya tarihi ya nuna cewa ta samo asali ne daga wani Basaraken Habe mai suna Sarkin kwaya, wanda ke mulki a wani gari da ake kira kwaya, da ke kudu da birnin jihar Katsina.

Aikin da yake yi wannan Basarake shi ne, sama wa Sarki hatsi, kamar irinsu su dawa da gero da sauransu, domin amfanin gidan Sarkin a wan nan lokaci.

An ce, ta ita wannan kofar kwaya ce Wali Jodoma, wanda Sarkin Katsina na lokacin ya kora, ya bi ya fita ya bar jihar katsina

Tarihi ya nuna cewa, ta wannan kofar Waliyyin ya fita, sai ya juya baya ya tsine ma wannan kofar ya ce, “ba za a taba yin wani abin kirki a kofar ba, sai bayan karni guda.

Ga yadda Katsinawa ke cewa, kusan kowace kofa ta samu ci gaba aman banda kofar kwaya.

To, amma yanzu din nan, da take ci gaba karni guda ne ya cika.

Ita ma wannan kofar, ana jin cewa a karni na 15 ne aka gina ta.

Ita ce yanzun xaka iya bi kaje Dutsinma, Runka, Kankara, Funtua Zaria, kaduna, Abuja da Sauransu.