Ƙofar Marusa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Kofar Marusa)
Kofar Marusa
Kofar_Marusa_Gate_Katsina
Kofar_Marusa_Gate_Katsina

Kofar Marusa tana ɗaya daga cikin kofofin dake cikin birnin Katsina.Ta kofar ne Marusan katsina y biyo zuwanshi katsina.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An gina kofar Marusa a wajen karni na Shabiyar 15 ne. Lokacin da aka gina sauran ganuwowin jihar Katsina, kuma ta samo asalin sunanta ne daga wani Basarake na Habe da ke mulkin Dutsi a wannan lokacin, wanda ake kira da Marusa Usman. Ta wannan kofar ce Marusa din ke bi in zai tafi Dutsi, ta nan ne kuma yake shiga idan ya dawo. Daga nan ne aka sanya ma kofar sunan Basaraken ta zama kofar Marusa Usman. Kofar Marusa, ta yi makwabtaka da wasu unguwanni da ke cikin kofar.

Wasu Unguwannin da kofar take[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai dai unguwar Kerau daga cikin ta wanda shekarunta ba su wuce sitinba 60 da kafuwa ba, koda yake, a da can, tun lokacin mulkin Habe har ya zuwa na Dallazawa, an yi wani wuri da ake kira unguwar Dantura, wanda a halin yanzu babu wannan unguwa saboda Kerau ta hade ta, ta koma cikin Kerau din. Sai ita kanta kofar marusan da sauransu...

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]