Kogin Zamfara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kogin Zamfara
General information
Labarin ƙasa
Map
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa 12°02′02″N 4°02′23″E / 12.03395°N 4.039681°E / 12.03395; 4.039681
Kasa Najeriya
Kogin Sokoto, kogin Zamfara zuwa kudu

Kogin Zamfara kogi ne a yankin arewacin Najeriya. Asalinsa daga jihar Zamfara, yana tafiyar kimanin 250 kilometres (160 mi) yamma zuwa cikin Jihar Kebbi inda ya haɗu da Kogin jihar Sakkwato kimanin 50 kilometres (31 mi) kudu maso yammacin Birnin Kebbi.

A mafi girman matsayinsa Kogin Zamfara yana ratsawa ta wani yanki mai 188 metres (617 ft) sama da matakin teku. Akwai sunaye daban-daban na Zamfara a yankuna daban-daban da yake ratsawa ta cikinsu. Wasu daga cikin wadanda suka shahara sun hada da: Gulbi Gindi, Gulbi Zamfara, Kogin Zamfara, da Kogin Gindi. Kogin yana a latitude 12 ° 2'2.22 "da kuma longitude: 4 ° 2'22.85" [1]

Jihar Zamfara, wacce a cikinta ne Kogin Zamfara ya samo asali.
Taswirar da ke nuna babban kogin Najeriya.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 

  1. "River Zamfara". Retrieved 23 October 2013.