Jump to content

Kungiyar Ma'aikatan Gambiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kungiyar Ma'aikatan Gambiya
labor union (en) Fassara
Bayanai
Farawa 1956
Ƙasa Gambiya

Kungiyar Ma'aikatan Gambiya, ana takaita sunan ƙungiyar da (GWU), babbar ƙungiya ce a cikin ƙasar ta Gambiya.

M.E. Jallow ne ya kafa GWU a shekarar 1956, Kuma shine Sakatare Janar na farko na ƙungiyar. Ƙungiyar ta yi rajista a hukumance a watan Yulin shekarar 1958. Da farko an shirya haɗa ma'aikatan ɓangaren gine-gine, ƙungiyar ta girma a ƙarshen shekarun 1950 bayan nasarorin da aka samu tare da ma'aikatan tashar jiragen ruwa waɗanda suka sami ingantaccen albashi da karin alawus.[1]::177 A shekara ta 1959, ƙungiyar ta haɗu da Kungiyar Kwadago ta Gambiya (GLU), kodayake an soke wannan gamin-bizar jim kaɗan bayan haka saboda bambance-bambance game da 'yancin kai da alaƙar ƙungiyar Kwadago ta Duniya.[2] A shekara ta 1977, gwamnatin ƙasar ta janye takardar izinin shaidar rajistar ƙungiyar bayan gazawar gabatar da asusun ƙungiyar ga gwamnatin.[1]:193

  1. 1.0 1.1 Perfect, David (1986). "Organized Labour and Politics in The Gambia: 1960-85". Labour, Capital and Society / Travail, Capital et Société. 19 (2): 168–199. ISSN 0706-1706. JSTOR 43157755.
  2. Blackburn, Daniel, ed. (2016). Trade unions of the world (7th ed.). London: International Centre for Trade Union Rights. p. 192. ISBN 978-0-9933556-1-5.