Jump to content

Kungiyar Malamai ta Tanzaniya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kungiyar Malamai ta Tanzaniya
labor union (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Tanzaniya

Kungiyar Malamai ta Tanzaniya, (ana takaita sunan da TTU), ƙungiya ce ta malamai a ƙasar ta Tanzaniya.

An kafa ƙungiyar ne a 1993 da niyyar bayar da shawarwari da inganta haƙƙin malamai a faɗin ƙasar ta Tanzaniya.

A shekara ta 2006, Shugaba Jakaya Kikwete ya naɗa shugabar ƙungiyar Margaret Simwanza Sitta a matsayin Ministan Ilimi da Horar da Kwarewa.[1]

Kungiyar tana da matsayi a taron koli na 17 na Tarayyar Afirka a shekara ta 2011. [2]

A cikin shekara ta 2012, malamai dubu 200,000 sun shiga yajin aiki bayan kashi 95.7 cikin dari na membobin Tarayyar kungiyar sun kaɗa kuri'a bisa wani dalilin. Shugaban ƙungiyar Gratian Mukoba ya ce ya zama dole a ƙara albashi.[3]

A watan Mayun 2017, ƙungiyar ta yi Allah wadai da korar ma'aikatan gwamnati dubu 10,000.[4]

Leah Yanya ita ce shugabar ƙungiyar ta yanzu.[5] Christopher Banda shine Mataimakin Shugaban ƙungiyar.

Ezekiah Oluoch ya kasance mataimakin sakatare janar na ƙungiyar.[6][7]

  1. International, Education (24 January 2006). "Tanzania: TTU President turns Education Minister". Education International (in Turanci). Retrieved 2020-05-26.
  2. "List of Observer Organizations at the African Union Summit". blog. Ministry of Information for Equatorial Guinea. Retrieved 1 July 2011.[dead link]
  3. "Tanzanian teachers in strike over pay". Reuters (in Turanci). 2012-07-30. Retrieved 2020-05-26.
  4. Kimani, Geofrey (4 May 2017). "Tanzania Teachers Union Condemns Civil Servants Sacking". AllAfrica. Retrieved 26 May 2020.
  5. Chibwete, Rachel; Mkiramweni, Nazael (2018-08-01). "Tanzania: PSSSF Fully Operational As Board Named". allAfrica.com (in Turanci). Retrieved 2020-05-26.
  6. "Court nullifies removal of Tanzania Teachers Union's Ezekiah". The Citizen (in Turanci). Retrieved 2020-05-26.
  7. Reporter, The Citizen (2020-02-13). "Tanzania: Court Nullifies Removal of Tanzania Teachers Union's Ezekiah Oluoch". allAfrica.com (in Turanci). Retrieved 2020-05-26.

Hanyoyin hadi na Waje

[gyara sashe | gyara masomin]

Karin Karatu

[gyara sashe | gyara masomin]