Kungiyar Taimako ta Buenos Aires
| Bayanai | |
|---|---|
| Iri | ma'aikata |
| Ƙasa | Argentina |
Sociedad de Beneficencia de Buenos Aires, wadda aka kuma sani da Sociedad de Damas de Beneficencia ko kuma a taƙaice Sociedad de Beneficencia (a Turanci: Society of Beneficence),[1] wata cibiyar gwamnati ce ta Argentina. Shugaba Bernardino Rivadavia ne ya kafa ƙungiyar a shekarar 1823. Manufarta ita ce mayar da ayyukan jin daɗin jama’a daga hannun Cocin Katolika zuwa ƙungiyar bayan samun ’yancin kai na Argentina.
Mercedes de Lasala de Riglos, wadda ta fito daga babban gidan sarauta, ita ce shugabar farko.[2] Mata ’yan ƙasar Argentina masu hannu da shuni daga manyan azuzuwan al’umma ne suke gudanar da ƙungiyar. Daga cikin waɗanda suka kafa ta akwai Mariquita Sánchez, wadda ta shugabanci ƙungiyar tsakanin 1830–1832 da kuma 1866–1867, María Cabrera de Altolaguirre, Isabel Casamayor, Joaquina de Izquierdo, Josefa Ramos Mejía, Isabel Agüero de Ugalde, Cipriana Viana de Boneo, Manuela Aguirre, María de los Santos Riera del Sar, Bernardina Chavarría de Viamonte da María del Rosario Azcuénaga.
Daga cikin cibiyoyin da aka sanya ƙarƙashin kulawar ƙungiyar akwai makarantun ’yan mata, asibitoci da gidajen marayu, kamar Casa de Niños Expósitos, Hospital Rivadavia da Casa de Huérfanas.
A shekarar 1838, gwamnan Buenos Aires, Juan Manuel de Rosas, ya dakatar da tallafin kuɗi daga gwamnati ga Sociedad de Beneficencia. Ba a sake kafa ƙungiyar a hukumance ba sai bayan ƙarshen mulkin Rosas a shekarar 1852.[1] A rabin na biyu na ƙarni na 19, Sociedad de Beneficencia ta gudanar da makarantu daban-daban na ’yan mata, asibitocin mata, cibiyoyin kula da masu tabin hankali da gidajen yari. Ƙungiyar ta kuma ba da gudummawa ga ayyukan agaji da asusun tallafa wa waɗanda suka shiga cikin matsala a wajen Buenos Aires.
An rusa Sociedad de Beneficencia a lokacin shugabancin farko na Juan Perón a shekarar 1947, bayan shugabannin ƙungiyar sun ƙi gayyatar matarsa, Eva Perón. A al’adance, wakilin Paparoma a Argentina da Uwargidan Shugaban Ƙasar Argentina ne ke zama shugabannin ƙungiyar, amma ƙungiyar ta ƙi gayyatar Evita bayan an zaɓi mijinta a matsayin shugaban ƙasa. Da farko, sun dage cewa dalilin hakan shi ne kasancewarta matashiya; amma mutane da dama sun ɗauki hakan a matsayin cin mutunci ga sabuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa. Evita ta fusata kuma ta ɗauki mataki a kan ƙungiyar, wanda a zahiri ya kawo ƙarshen ayyukanta. Daga nan ta kafa Eva Perón Foundation domin maye gurbin ta, wadda ita da kanta ta gudanar kuma ta fi ta faɗin ayyuka.[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Shumway, Jeffrey M. (2019). A Woman, a Man, a Nation: Mariquita Sánchez, Juan Manuel de Rosas, and the Beginnings of Argentina. Albuquerque: University of New Mexico Press. p. 118. ISBN 978-082-636-091-5. Retrieved 12 October 2022 – via Google Books.
- ↑ García López, Ana Belén (2016-11-07), Las heroínas silenciadas en las independencias hispanoamericanas (in Sifaniyanci), Megustaescribirlibros, ISBN 978-84-9112-679-9, retrieved 2017-11-30
- ↑ OSPAT (2017-04-18). "La sociedad de beneficiencia: inicio y culminación". OSPAT (in Sifaniyanci). Retrieved 2020-04-17.