Jump to content

Kungiyar yaki da tauye hakkin mata

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Shirin Yaki da Tauye Hakkin Mata, kungiyar ce wacce a turance Ake Kira da (No to Oppression against Women Initiative)3 da harshen Larabci ana Kiran ta da, (Larabci: مبادرة لا لقهر النساء Mubādirat Lā Liqahr al-Nisā’)4, ƙungiya ce ta kare haƙƙin mata daga ƙasar Sudan. Ƙungiyar ta kasance mai aiki a lokacin mulkin Omar al-Bashir2 kuma ta taka muhimmiyar rawa a yayin Juyin Juya Halin Sudan na shekarun 2018–2019.3

An samar da shirin Yaki da Tauye hakkin mata a shekara ta 2009 don kare hakkin mata a Sudan bayan da aka kama Lubna Ahmed al-Hussein, wata 'yar jarida 'yar kasar Sudan da ke aiki tare da Majalisar Dinkin Duniya, da laifin sanya wando, wanda hukumomin shari'a suka dauka a matsayin cin zarafi da ya saba wa dokokin shari'a. An kama Hussein ne tare da wasu mata guda goma sha biyu wadanda su ma suka sa wando a wani gidan cin abinci na Khartoum. A shari'ar da aka yi a ranar 4 ga watan Agustan 2009, mata da maza dari biyu sun yi zanga-zangar nuna adawa da shari'ar kuma 'yan sandan kwantar da tarzoma sun tarwatsa ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye, garkuwa da sanduna. An riga an yi wa mata goma bulala saboda sanye da wando. Ɗaya daga cikin tutocin zanga-zangar a zanga-zangar 4 ga Agusta ta nuna taken da aka ɗauka a matsayin sunan Ƙaddamarwa: "Ba za a zalunce mata ba"[5].

Mambobin Kungiya

[gyara sashe | gyara masomin]