Jump to content

Kwalejin Rumfa Kano

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kwalejin Rumfa wata makarantar sakandare ce da ke Arewa Najeriya a Jihar Kano, An kafa ta a shekarar 1927 a matsayin Makarantar matakin Tsakiya ta Kano (sa'an nan kuma ta canza zuwa Makarantar Lardin Kano), daga baya aka sake masa suna zuwa Kwalejin Gwamnati ta Kano, kuma yanzu ana kiranta Kwalejin rumfa, Kano . Sunan Rumfa ya fito ne daga sunan Muhammad Rumfa . [1]

Kwalejin Rumfa, awani lokaci ɗaya daga cikin manyan makarantun kwana a Arewacin Najeriya, ba ta aiki a matsayin makarantar kwana. An san makarantar da adadi mai yawa daga cikin fitattun mutane daga yankin da suka halarceta. Tsoffin ɗalibanta sun haɗa da Janar Sani Abacha da Janar Murtala Mohammed waɗanda suka kasance tsoffin Shugabannin Najeriya, Dokta Ado Bayero sarkin Jihar Kano, Gwamnan Jihar Jigawa Mohammed Badaru Abubakar, tsohon gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar , tsohon shugaban Bankin Unity plc Nu'uman Barau Danbatta

Shahararrun ɗalibai

[gyara sashe | gyara masomin]

Shahararrun tsofaffin ɗaliban Rumfa sun haɗa da:

  1. "Muḥammad Rumfa | king of Kano". Encyclopedia Britannica (in Turanci). Retrieved 2021-01-15.
  2. Focus, Kano. "RUMFOBA to grant scholarship to 20 students of Rumfa College" (in Turanci). Archived from the original on 2021-04-11. Retrieved 2021-01-15.
  3. "Barau Danbatta, Unity Bank PLC: Profile and Biography". Bloomberg.com (in Turanci). Retrieved 2021-01-15.