Jump to content

Kwaw Ampah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kwaw Ampah
Member of the 2nd Parliament of the 1st Republic of Ghana (en) Fassara

9 ga Yuni, 1965 - 24 ga Faburairu, 1966
Election: 1965 Ghanaian parliamentary election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Kogin Zinariya (Mulkin mallaka na Birtaniyya)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Kiristanci

Kwaw Ampah, wanda kuma aka fi sani da suna Joseph Kwaw Ampah ɗan kungiyar kwadagon Ghana ne kuma ɗan siyasa. [1] An, naɗa shi babban sakataren jam'iyyar Trade Union Congress (TUC) ta gwamnatin jam'iyyar Convention People's Party a watan Yunin 1964 ta maye gurbin Magnus George. [2] Kafin naɗin nasa, ya kasance sakataren kungiyar ma'aikatan gwamnati. A shekarar 1965 shi da wasu ’yan kwadagon da suka haɗa da John Tettegah wanda a lokacin shi ne babban sakatare na kungiyar kwadago ta Afrika baki ɗaya ya zama ‘yan majalisa masu wakiltar jam’iyyar Convention People’s Party. [3] Kwaw Ampah ya kasance ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Juabeso-Bia daga shekarun 1965 zuwa 1966 lokacin da aka hambarar da gwamnatin Nkrumah. [4] [5] Ya riƙe wannan ofishin ne a matsayin babban sakatare na TUC.

  • Jerin sunayen 'yan majalisar da aka zaba a zaben 'yan majalisar dokokin Ghana na 1965
  1. "Ghana Year Book 1970–1971". Ghana Year Book. Daily Graphic: 73. 1971.
  2. "News from Hsinhua News Agency: daily bulletin". News from Hsinhua News Agency. Xin hua tong xun she, London: 39. 16 September 1965.
  3. "Africa Report, Volume 10". African-American Institute. 1965: 8. Cite journal requires |journal= (help)
  4. "West Africa Annual, Issue 8". West Africa Annual. James Clarke: 80. 1965.
  5. "Parliamentary Debates; Official Report, Part 2". Ghana National Assembly. 1965: iii. Cite journal requires |journal= (help)