Jump to content

Laylah Ali Othman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Laila Ali Othman)
Mukala mai kyau
Laylah Ali Othman
Rayuwa
Haihuwa Jihar Yobe, 29 ga Janairu, 1986 (40 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
ESCAE-University, Benin (en) Fassara
Harsuna Hausa
Turanci
Pidgin English (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa, marubuci da mai gabatarwa a talabijin

Laylah Ali Othman(an haife ta a ranar 29 ga watan Janairu shekarata alif dubu daya da dari Tara da tamanin da shida (1986)) yar Najeriya ce wace aka fi sani da yin sana’ar sayar da kayan gyaran gida kamar kujeru da gadaje[1].Ita mawallafiya ce, kuma kuku ce[2],sanan kuma itace mamallakin kamfanin buga mujallar da ake kira L magazine, tana kuma gabatar da shiri da ake kira Voices of the Youth[3].

Farkon Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifa Laylah a jihar yobe[4], ammata tashi ne a Kaduna, inda tayi rayuwar ta a jihar Kaduna, inda tayi karatun ta na nursery da firamare a cikin Jihar Kaduna, Bayan kuma ta yi makarantar sakandire ta Junior & Senior a Damaturu. A halin yanzu ita ce Shugaba kuma Manajan Darakta na Superb rb , wato &N (Laylah & Nahaar) Interiors and Exterior Décor Nig[5].

Ta na da Digiri a fannin harshen Ingilishi daga [6] Jami'ar Maiduguri, Diploma a interior decoration daga Lotus Educational Institute, Dubai da wani diploma kuma a space management daga Maren School of Interior Décor and Design, bugu da ƙari ta ƙara digiri na biyu a jami’ar ESAE dake ƙasa Benin Republic.

tayi aure Sau biyu auren na mutuwa.

Layla Ali othman ita ce ta ƙirƙiro da wani ƙungiya mai zaman kanta mai suna Laylah Initiative for the Boy and Girl Child Charity Foundation (LIBGC); ƙungiya ce da'ake ba da kulawa ga al-Manifī'', da kuma basu ilimi kyauta a wani rukuni na ɓangaren yaran da ke cikin buƙata, kamar Almajiri' da sauran ƙananan yara marassa galihu, ta hanyar shirin talabijin da ake kira Laylah's Way, inda take taimakan talakawa da kuma sauran jama'a, tana amfani da wanan shirin don taimakawa mutanen da ba zasu iya samun saukin rayuwa ko samun rayuwa mai kyau ba, ta hanyar basu cikakkiyar kayan gida[8].

Daga baya ta zama mai gabatar da shiri wanda ake kira Voices of the Youth. A cikin wannan shiri, ta bayar da damar samar da ingantacciyar rayuwa ga marasa galihu, da kuma karfafama mutane gwiwa game da yadda za su zama ƴan kasuwa, tare da koya masu ilimin yadda ake gina ingantaccen hanyar samun kuɗi, da kuma magance matsalolin da matasan Najeriyar ke fuskanta a yayin da suke ƙoƙarin samun ci gaba da nasara a rayuwarsu[9].

Bayan nasarorin da ta samu a kafafen yaɗa labarai, ita ce mai gabatar da shirin talabijin da ake kira Muryar Jama’a, shirin wasa ne wanda ke nuna rayuwa da al'adun Hausawa, Ita kuma ta mallaki kamfanin L Magazine, mujallar ce da ke nuna abubuwan kaman kayan ado na cikin gida, kiwon lafiya da salon rayuwa; ita ce marubuciya na Something Deep da Masked[10].

Lambobin yabo da nasarori

[gyara sashe | gyara masomin]
ShekaraLambar yaboKungiyar
2018Award of ExcellenceGamji Students
2015Award of HonorEastern Mediterranean University (Nigerian Week)
2018Award of ExcellenceDepartment of Public Admin, Faculty of Admin, ABU
2018Award of ExcellenceWest African Students
2019Meritorious Award of HonorNigerian Youth Progress in Democracy
2019Certificate of HonorDemocratic Youth Assembly of Nigeria
2018Certificate of Appreciation[permanent dead link]Startup Sokoto
2018Certificate of ParticipationStartup Kano
2019Award of HonorNational Association of Nigerian Students (Zone A)
2019Life Time Award of CredenceYouth Assembly of Nigeria
2019Northern Philanthropic Award of ExcellenceSave Democracy Group, Africa
2020Award of HonorNational Association of Northern Corpers[11]
2019Corporate Social Responsibility AwardPR Times Africa[permanent dead link]
  1. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49865877?ocid=wshausa.chat-apps.in-app-msg.whatsapp.trial.link1_.auin
  2. http://www.landnkitchen.com/
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-04-22. Retrieved 2020-05-19.
  4. https://www.youtube.com/watch?v=CGkA-Onzamc
  5. http://www.superblandninteriors.com/[permanent dead link]
  6. http://www.citypeopleonline.com/meet-the-young-female-entrepreneurs-rocking-abuja/
  7. https://hausa.legit.ng/1263425-bayan-aurena-ya-mutu-sau-biyu-mutane-suna-ta-zargin-cewa-lalacewa-zanyi-laila-ali-othman.html
  8. https://www.youtube.com/watch?v=RxDy0lXAY2A&feature=youtu.be
  9. http://www.citypeopleonline.com/meet-the-young-female-entrepreneurs-rocking-abuja/
  10. https://www.youtube.com/watch?v=CGkA-Onzamc
  11. https://www.youtube.com/watch?v=CGkA-Onzamc