Jump to content

Lalla Lamia Al Solh

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lalla Lamia Al Solh
Rayuwa
Haihuwa Berut, 4 ga Augusta, 1937 (87 shekaru)
ƙasa Lebanon
Ƴan uwa
Mahaifi Riad Al Solh
Abokiyar zama Prince Moulay Abdallah of Morocco (en) Fassara
Yara
Ahali Mona Al Solh (en) Fassara da Leila Al Solh (en) Fassara
Yare 'Alawi dynasty (en) Fassara
Karatu
Makaranta University of Paris (en) Fassara
Sana'a

Gimbiya Lalla Lamia ta Maroko (Larabci; an haife Lamia Al Solh, ranar 4 ga watan Agustan shekara ta alif 1937) [1] haifaffiyar kasar Lebanon ce daga dangin masarautar Maroko. Ita ce matar mamaci Yarima Moulay Abdallah na Maroko kuma mahaifiyar Gimbiya Lalla Zineb da Yarima Moulay Hicham da Moulay Ismail.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife ta a Lebanon a ranar 4 ga watan Agustan shekara ta 1937, Lamia ita ce ta biyu cikin 'ya'ya mata biyar na Riad Al Solh, Firayim Ministan kasar.[2] Lokacin da take 'yar shekara 14 a duniya, an kashe mahaifinta a wani hari da mambobin Jam'iyyar Socialist ta Siriya suka kai.[1] Ta yi karatu a jami'ar La Sorbonne da ke birnin Paris kuma ta kammala karatu a 1959 ta samu digiri na farko a harshen Faransanci da adabi. [2][3][4]

Ta yi aiki a matsayin jagora a kungiyar Alaouite don inganta rayuwar makafi a Maroko (OAPAM) tun lokacin da aka kirkireshi a shekarar 1967. [5][6]

Lamia ta hadu da wanda zai zamo mijinta na gaba Yarima Moulay Abdallah a Paris a shekara ta 1957, yayin da take daliba a La Sorbonne. An masu baiko a Beirut a ranar 5 ga Nuwamba 1959.[7][8] An yi daurin auren ne a Rabat, a ranar 9 ga Nuwamba 1961, a cikin bikin aure biyu tare da Latifa Amahzoune, amarya ta surukinta Sarki Hassan II. Bayan ta shiga cikin dangin sarauta, ta zamo Lalla Lamia kuma Hassan II ya ba ta taken Gimbiya da kuma taken Mai Girma.[9][5] Sun sami 'ya'ya uku daga ta hanyar wannan aure:

  • Yarima Moulay Hicham (4 Maris 1964);
  • Gimbiya Lalla Zineb (1971);
  • Yarima Moulay Ismail (1981).
  • 4 ga Agustan 1937 - 9 ga Nuwamba 1961: Budurwa Lamia Al Solh
  • 9 Nuwamba 1961 - yanzu: Mai Girma Gimbiya Lalla Lamia
  1. 1.0 1.1 Lazkani·Histoires·, Souad (2021-02-17). "L'histoire de la Libanaise qui a épousé un prince marocain" (in Faransanci). Retrieved 2024-04-11. Cite error: Invalid <ref> tag; name "Lazkani·Histoires·" defined multiple times with different content
  2. 2.0 2.1 Matnawi. Journal D'un Prince Banni - Moulay Hicham (in English). p. 13. Retrieved 2024-04-11.CS1 maint: unrecognized language (link)
  3. Actes du XVIIe Congrès international de sociologie, Beyrouth 23-29 septembre 1957 (in Faransanci). Pub. avec l'aide fu gouvernement libanais par les soins du Comité d'organisation. 1958. p. 726.
  4. Paris-match (in Faransanci). Paris-Match. 1961. p. 29.
  5. 5.0 5.1 "Hommage à Rabat à SA la Princesse Lalla Lamia Essolh – O.A.P.A.M" (in Faransanci). Retrieved 2024-04-11. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content
  6. diplomatique, Maroc (2023-12-02). "Hommage à Rabat à SA la Princesse Lalla Lamia Essolh en reconnaissance de son action en faveur des non et malvoyants". Maroc Diplomatique (in Faransanci). Retrieved 2024-04-11.
  7. Legum, Colin (1962). Africa; a Handbook to the Continent (in Turanci). Praeger. p. 47.
  8. "Lebanese Princess Lamia El Solh And Her Fiance Prince Abdallah Of..." Getty Images (in Turanci). 2010-11-04. Retrieved 2024-04-15.
  9. "Mohamed Cherkaoui, la princesse Lalla Malika, la princesse Lalla..." Getty Images (in Turanci). 2016-01-19. Retrieved 2024-04-11.