Lamaba Tubani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Lamaba Tubani Abincin gargajiya ne, mai daɗaɗɗen tarihi.[1]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Abincin na gargajiya ne, wanda ya yi daruruwan shekaru da sanuwa kuma ya shahara a arewacin najeriya musamman yankin arewa maso gabas, ya shahara sosai a wurin kabilar kare kare dama sauran kabilunda sukeda dangan taka da ita wanda har akan iya musulaƙabi dacewa shine abincin yarensu, sunayin shine acikin ganyen dawa wacce akekira da (sharam) kokuma a daurasa a leda.[2]

Yayinda yankin arewa maso gabashin Nigeria suke ƙiransa da tubani su kuma suna yinsa aleda kokuma ganye yanayi ga duk wanda ya samu, haɗinsa kuma duk kusan ɗaya ne banbanci kawai sai dai abinda ya zama ba dole sai anyi amfani dashi ba.

Kayan haɗi[gyara sashe | gyara masomin]

Garin masara kokuma garin dawa wasu sukan iya qarawa da filawa sanda asa Wake dakuma Karkashi, kanwa Jihohinn da sukafi shahara wajenyi da sunan da suke kira

  • Yobe lamba
  • Bauchi lamba
  • Kano tubani
  • Kaduna tubani

Amfanin shi[gyara sashe | gyara masomin]

DAyake yana tattare da kayan hadi iri daban kusan kowanne yanada amfani na musamman ga lafiyar dan adam kamar fulawa yana kara hasken ido dayake yana tattare da bitamin A, sannan wake furotin ne shikuma masara da dawa carbohydrate ne

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://cookpad.com/ng/recipes/6474822-lamba
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-01-18. Retrieved 2022-01-17.