Lambar tantance dan kasa nada matukar muhimanci ga duk 'yan Najeriya
Gwamnatin kasar Najeriya, da mahukuntan kasar sun bada umurnin cewar tun daga farkon shekara ta dubu biyu da Shatara (2019), dole ne kowane dan kasa ya samu lambar shaidar zama dan kasa, idan suna so su more wasu abubuwa wadanda ake samu daga ma'aikatu da hukumomin gwamnati.[1]
Umarni
[gyara sashe | gyara masomin]Wannan umurni bai yi wa wasu 'yan kasa dadi ba, Shugaban Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa Reshen Arewa Maso Gabas, Saleh Bakoro Sabon Fegi Damaturu, wanda ya ce hukumar ba ta yi dai-dai ba, yana ganin tsoro ta ke ji kar a sa ido akan ayyukan ta, shi ne ya sa ta fito da wannan batu na samun lambar zama dan kasa.[2][3]
Yana mai cewa a baya ma hukumar ta ce a yi katin zama dan kasa wanda har yanzu shekaru 12 kenan ba a kamalla aikin ba, ganin cewa cibiyoyin rajista 1,000 ne kawai hukumar ta bude wa 'yan kasa sama miliyan 185.
Jawabi
[gyara sashe | gyara masomin]A jawabinsa, Shugaban Hukumar bada katin zama dan kasa Injiniya Aliyu Aziz Abubakar, ya ce Najeriya ce kasa ta 7 mai yawan mutane a duniya, kuma ita ce ba tada kuma tsarin wannan lambar ta zama dan kasa, ya ce idan ana so a yi tsare-tsare da al'umma za su samu romon mulkin da ake yi, lallai dole ne a samu wannan lambar da kuma katin zama dan kasa.
Yawancin abubuwa da ke bukatan wannan lambar sun hada da harkar kiwon lafiya, makaranta, mallakan filaye da dai sauransu.
Tasiri
[gyara sashe | gyara masomin]Wannan tsari na lamba da kuma katin zama dan kasa zai baiwa Gwamnati damar sanin su waye 'yan kasa, kuma suwaye bakin haure, zai kuma bada damar sanin mutane mawa ke morewa shirye shirye da tsare tsare da gwamnatin ke yi domin talakawanta.